Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Inzali - Tana nufin gamsuwar jima'i.
Misali;Lalurar sanyi na sanya saurin inzali ga ma'aurata.
ENG; Orgasm (A turance tana nufin inzali)
Iri - Tana nufi abin da ake shukawa.
Misali;Iri ya yi tsada yanzu shi yasa manoma ke kokawa.
ENG; Seed (A turance tana nufin iri)
Ishara - Tana nufin nuni ko alama.
Misali; Duk wanda ya yi mugunta sai ya ga ishara kafin ya mutu.
ENG; Sign/Indication (A turance tana nufin ishara)
Ishirin - Tana nufin goma sau biyu.
Misali; Kaji guda ishirin ya siyo don gudanar da bikin.
ENG; Twenty (A turance tana nufin ishirin)
Iska - Tana nufin abin da ke kaɗawa kuma ababen halitta ke shaƙa don su rayu.
Misali; Tun safe iska mai sanyi take kaɗawa yau.
ENG; Air (A turance tana nufin iska)
ISlamic Medical Association of Nigeria (IMAN) - Ƙungiyar Likitoci Musulmai Ta Najeriya
Istihara - Tana nufin neman zaɓin Allah.
Misali; Ya kamata ki yi istihara a tsakanin masu neman auren ki.
ENG; Seeking Devine Counsel (A turance tana nufin istihara)
Itace - Tana nufin bishiya.
Misali; Wannan itacen ɗorawa ne.
ENG; Tree (A turance tana nufin bishiya)
Iyaka - Tana nufin ƙarshe.
Misali; Komai na Allah yana da iyaka kuma iyakokin Allah su ne abin kiyayewa.
ENG; Boundary (A turance tana nufin iyaka)
Iyali - Tana nufin ahali ko kuma uwa da uba da yaransu.
Misali; Yana kula da iyali yanda ya kamata.
ENG; Family (A turance tana nufin iyali)