Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Uproot - A turance tana nufin ɓaɓɓake.
Misali; Ya ɓaɓɓake bishiyar daga ƙofar gidansa.
HAU; Ɓaɓɓake (Tana nufin jijjige abu daga tushensa)
Uproot By Shaking - A turance tana nufin girgiɗe.
Misali; An girgiɗe mata haƙorin don ya ishe ta da ciwo.
HAU; Girgiɗe (Tana nufin cire abu da ƙarfi)
Urine - A turance yana nufin bawali.
Misali; Ya yi bawali a ƙofar makaranta.
HAU; Bawali (Tana nufin fitsari)
Urine - A turance tana nufin fitsari.
Misali; Amir ya yi fitsari a jikinsa.
HAU; Fitsari (Tana nufin wani ruwa da jiki ba ya buƙata wanda ke fitowa daga ƙoda)
Usefulness - A turance tana nufin fa'ida.
Misali; Zumunci yana da fa'ida don yana sa albarka a rayuwa.
HAU; Fa'ida (Tana nufin amfanin abu)
Kishiyarta; Rashin Fa'ida
Utterance - A turance tana nufin furuci.
Misali; Yana da furuci daddaɗa.
HAU; Furuci (Tana nufin yin magana)
Uwar Garke - Babbar ƙafa ko garken da yake ba wa sauran kafafen intanet damar shige da fice domin samun bayani.
Uwar Kudi - Jari ko tsagwaron kudin da ake juyawa a harkar kasuwanci.