Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Nose - A turance tana nufin hanci.
Misali; Ƙurji ya fito mata a saman hanci mai ɗan karen ciwo.
HAU; Hanci (Tana nufin gaɓar da ake numfashi wadda take a saman baki)
Nose-bleed - A turance tana nufin haɓo.
Misali; Tun safe yake haɓo, ko za a kai shi asibiti ne?
HAU; Haɓo (Tana nufin zubar jini daga hanci)
November - A turance yana nufin wata na goma sha ɗaya.
Misali; Watan Nuwamba yana da kwana talatin a kowacce shekara.
HAU; Nuwamba (Wata ne na goma sha ɗaya a shekara)
Nursing - A turance tana nufin jinya.
Misali; Ya shekara guda yana jinya sakamakon haɗarin.
HAU; Jinya (Tana nufin kwanciya a dalilin rashin lafiya ko kula da mara lafiya)
Nutty Flavour - A turance tana nufin garɗi.
Misali; Madarar tana da garɗi sosai.
HAU; Garɗi (Tana nufin wani nau'in ɗanɗano mai daɗi a baki)
Nuwamba - Wata ne na goma sha ɗaya a shekara.
Misali; Watan Nuwamba yana da kwana talatin a kowacce shekara.
ENG; November (A turance yana nufin wata na goma sha ɗaya)