Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Need - A turance tana nufin buƙata. Misali; Ina buƙatar kwanaki masu yawa kafin na kammala wannan aikin. HAU; Buƙata (Tana nufin abinda  ake muradi ko ake so)
Neighing - A turance tana nufin haniniya. Misali; Dokunan suna ta haniniya tun safe. HAU; Haniniya (Tana nufin kukan doki)
Net Bag - A turance tana nufin cali. Misali; A zuba tumaturan a cikin cali saboda kar ya lalace. HAU;Cali (Tana nufin jaka mai raga-raga)
New opportunities/ Progress - A turance tana nufin buɗi. Misali; Allah ya ƙara buɗi ga duk masu sauƙaƙawa talakawa. HAU; Buɗi (Tana nufin samun damammaki ko cigaba a kasuwanci ko karatu ko wasu al'amura)
New Partnership for Africa’s Development (NEPAD) - Gidauniyar Haɗin Guiwar Bunƙasa Sabuwar Afirka
News Agency of Nigeria (NAN) - Kamfanin Dillancin Labarai Na Najeriya
Newspaper - A turance tana nufin jarida. Misali; Dattijai na son karanta jarida don jin halin da duniya take ciki. HAU; Jarida (Tana nufi takarda mai ƙunshe da rubutun labarai)
Newspaper Proprietors Association of Nigeria (NPAN) - Ƙungiyar Mamallaka Kamfanin Jarida Ta Najeriya
Next year - A turance tana nufin baɗi. Misali; Auren sai baɗi za a yi shi. HAU; Baɗi (Tana nufin shekara mai zuwa)
Nigarian Instutite of International Affairs (NIIA) - Cibiyar Nazarin Hulɗar Jakadanci Ta Najeriya
1 12 13 14 15 16 31