Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Losing Baby Teeth - A turance tana nufin famfara.
Misali; Muntari yana famfara.
HAU; Famfara (Tana nufin cirewar da haƙoran yara ke yi kafin na girma ya fito)
Lost - A turance tana nufin ɓata.
Misali; Ina tunanin takalmin ya ɓata, don na duba ko ina ban ganshi ba.
HAU; Ɓata (Tana nufin a nemi abu a rasa)
Loud Argument - A turance tana nufin hatsaniya.
Misali; Mata da mijin sun yi hatsaniya har ta kai matar ta yi yaji.
HAU; Hatsaniya (Tana nufin cacar baki ko cece-kuce)
Low mud platform outside compound - A turance tana nufin dakali.
Misali; Baba yana zaune a kan dakali da abokinsa suna hira.
HAU; Dakali (Tana nufin gini mai ɗan tudu da ake yi a ƙofar gida don zama)
Lungs - A turance tana nufin huhu.
Misali; Shan taba yana illata huhu a wasu lokutan ma har a rasa rai.
HAU; Huhu (Tana nufin ɓangaren da ke sarrafa iska a jikin ɗan Adam)