Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Leaves or stalk of beans, groundnut etc - A turance tana nufin harawa.
Misali; Dabbobin na cinye buhun harawa biyu a mako guda.
HAU; Harawa (Tana nufin busasshen ganyen wake ko na gyaɗa da sauransu wanda ake ba wa dabbobi)
Left - A turance tana nufin hagu.
Misali; Da hannun hagu yake rubutu.
HAU; Hagu (Tana nufin ɓarin hagu a jikin ɗan Adam, idan aka kalli mutum daga sama zuwa ƙasa, ɓari ɗaya shi ne hagu ɗayan kuma dama)
Kishiyarta; Dama
Left handed person - A turance yana nufin bahago.
Misali; Ado bahago ne.
HAU; Bahago (Yana nufin wanda yake amfani da hannun hagu ko kuma mutum mai wuyar sha'ani)
Left-over Food - A turance tana nufin dago-dago.
Misali; Akwai dago-dago a ɗakin girki, a ba wa almajirai idan sun yi bara.
HAU: Dago-dago (Tana nufin ragowar abinci)
Leg / Foot -
A turance tana nufin ƙafa.
Misali; Ya ji ciwo a ƙafarsa sakamakon faɗuwa da ya yi a filin ƙwallo.
HAU; Ƙafa (Tana nufin sashen jikin mutum ko dabba da ake amfani da shi wajen tafiya)
Legal Aids Council of Nigeria (LACON) - Hukumar Tanyon Maƙaraya Ta Najeriya
Legion - Ƙungiya
Leken Asiri - Bibiyar al'amuran jama'a ko na wata kasa don gano wasu abubuwa na tsaro.
Leopard - A turance tana nufin damisa.
Misali; Akwai ƙaton hoton damisa a ƙofar fadar sarkin.
HAU; Leopard (Tana nufin dabbar daji mai cin nama)
Leper - A turance tana nufin kuturu.
Misali; Ya ba wa kuturu sadaka a hanyarsa ta zuwa kasuwa.
HAU; Kuturu (Tana nufin mai ɗauke da lalurar kuturta)