Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Large needle - A turance tana nufin basilla.
Misali; Na yi amfani da basilla na ɗinke buhun kayana.
HAU; Basilla (Tana nufin allura babba da ake amfani da ita wajen ɗinke buhu ko ƙwarya da sauransu)
Large Stallion - A turance tana nufin ingarma.
Misali; Dokin yarima ingarma ne.
HAU; Ingarma (Tana nufin babban doki ko gabjejen mutum)
Last Long - A turance tana nufin daɗe.
Misali; Yau ɗaliban sun daɗe ba a tashe su ba.
HAU; Daɗe (Tana nufin ɗaukan lokaci mai tsaho)
Last year - A turance tana nufin bara.
Misali; Bara ya cika shekara biyar da rasuwa.
HAU; Bara (Shekarar da ta gabata)
Last year’s kolanuts - A turance tana nufin daushe.
Misali; Gwaggo ta fi son goro daushe.
HAU; Daushe (Tana nufin tsohon goro)
Later - A turance tana nufin bisani.
Misali; An ɗauke min kuɗina amma daga bisani an dawo min da su.
HAU; Bisani (Tana nufin daga baya ko kuma bayan)
Laugh - A turance tana nufin dariya.
Misali; Jama'a na ta dariya sakamakon ganin ɗan wasan barkwancin da suka yi.
HAU; Dariya (Tana nufin canja yanayin fuska tare da bayyana haƙora sakamakon wani abin farin ciki ko nishaɗi)
Leader/Guide - A turance tana nufin ja-gaba.
Misali; Annabi SAW shi ne ja-gaban dukkan halitta.
HAU; Ja-gaba (Tana nufin shugaba ko jagora)
League - Hukuma, Ƙungiya
League Management Company (LMC) - Kamfanin Harkokin Wasanni