Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Jambaɗe - Tana nufin ƙurajen da ke fitowa a hammata masu zafi sosai.
Misali; Jambaɗe ne ya fito mata kuma ya zuba mata zazzaɓi mai zafi.
ENG; Abscess under armpit (A turance tana nufin jambaɗe)
Jamfa - Tana nufin rigar da ake sa wa a ƙasa kafin a ɗora babbar riga.
Misali; Ya sa jamfa mai gajeren hannu kalar makuba.
ENG; Long sleeve worn as inner garment (A turance tana nufin jamfa)
Jamhuriya - Tana nufin ƙasar da ke da tsarin mulki na musamman.
Misali; Jamhuriyar Niger ta ayyana Hausa a matsayin harshen da za a yi amfani da shi a ƙasar.
ENG; Republic (A turance tana nufin jamhuriya)
Jami’a - Tana nufin makarantar gaba da sakandire.
Misali; Gambo ya shiga jami'a ne a shekarar da ta gabata.
ENG; University (A turance tana nufin jami'a)
Jami’i - Ma'aikaci, musamman na gwamnati ko wata masana'anta da ya samu horo
Jan-baki - Tana nufin abin shafawa a leɓe mai canja masa launi wanda mata ke amfani da shi.
Misali; Amaryar ta sha ado da jan-baki.
ENG; Lipstick (A turance tana nufin jan-baki)
Jan-gwada - Tana nufin namijin ƙadangare.
Misali; Jan-gwada ne ya hana sauran ƙadangarun cin abinci.
ENG; Orange-headed male lizard (A turance tana nufin jan-gwada)
Jana’iza - Tana nufin sallar da ake yi wa mamaci kafin a kai shi kabari.
Misali; Za a yi jana'iza a babban masallacin Juma'a yau.
ENG; Funeral (A turance tana nufin jana'iza)
Janaba - Tana nufin rashin tsarki a addinin musulunci sakamakon biƙi, haila, kusantar iyali da sauransu.
Misali; idan mutum na da janaba, ba zai yi sallah ba dole sai ya yi tsarki.
ENG; Religious Impurity (A turance tana nufin janaba)
Kishiyarta; Tsarki
Janairu - Watan farko ne a shekara.
Misali; Bikin sabuwar shekara na kasancewa a ranar ɗaya ga watan Janairu.
ENG; January (A turance yana nufin watan farko a shekara)