Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Jugum - Tana nufin zama shiru tare da saƙe-saƙe ko tunani.
Misali; Tun da na shigo ta yi jugum a zaune.
ENG; Despondently (A turance tana nufin jugum)
July - A turance yana nufin wata na bakwai a shekara.
Misali; A watan Yuli zai cika shekara biyar da gama makaranta.
HAU; Yuli (Wata ne na bakwai a shekara)
Juma’a - Rana ce ta biyar a ranakun mako.
Misali; Yara na ɗokin zuwa masallaci ranar Juma'a.
ENG; Friday (A turance tana nufin rana ta biyar a mako)
June - A turance wata ne na shida a shekara.
Misali; Damina na kankama a watan Yuni.
HAU; Yuni (Wata na shida a shekara)
Jure - Tana nufin dauriya.
Misali; Ta jure mugayen halayensa tsawon shekaru.
ENG; Endure (A turance tana nufin jure)
Juya - Tana nufin rubuta abu kamar yanda yake.
Misali; Idan kin gama rubutun ki ba ni na juya.
ENG; Copy Something Written (A turance tana nufin juya)
Juyayi - Tana nufin alhini ko tausayi.
Misali; Muna cikin juyayi sakamakon rashin da muka yi.
ENG; Sympathy/Pity (A turance tana nufin juyayi)
Juyi - Tana nufin canjawa daga wani yanayi zuwa wani.
Misali; Indo ta zata naƙuda ta fara amma juyi ne.
ENG; Change of position (A turance tana nufin juyi)