Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Hutu - Tana nufin zama guri ɗaya ba tare da aikin komai ba ko rashin zuwa gurin aiki ko makaranta ko gyurin sana'a na wani lokaci don a tsahirta kafin a ɗora.
Misali; Yara ba sa zuwa makaranta saboda an ba su hutu.
ENG; Rest/Holiday (A turance tana nufin hutu)
Huɗu - Tana nufin lambar da ke bin bayan uku.
Misali; Musulunci ya ba wa maza damar auren mata guda huɗu.
ENG; Four (A turance tana nufin huɗu)
Huɗuba - Tana nufin jawabai na hikima da jan hankali don faɗakarwa ko kwaɗaitarwa a kan binn Allah da kuma gujewa saɓa masa.
Misali; Muna sauraron huɗuba daga masallaci mai alfarma a rediyo.
ENG; Sermon (A turance tana nufin huɗuba)
Hyena - A turance tana nufin kura.
Misali; Mafarautan sun kamo kura.
HAU; Kura (Tana nufin wata dabbar daji mai cin ɗanyen nama)