Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Hula - Tana nufin nau'in sutura da ake sa wa a kai. Misali; Ya sanya hula zanna bukar 'yar Maiduguri. ENG; Cap (A turance tana nufin hula)
Hulu-hulu - Tana nufin kumburi sosai. Misali; Idonsa ya yi hulu-hulu tun jiya saboda ciwo yake masa,. ENG; Swollen (A turance tana nufin hulu-hulu)
Hulɗa - Tana nufin mu'amala ko cuɗanya. Misali; An ƙulla hulɗar cinikayya tsakanin 'yan kasuwar. ENG; Transaction (A turance tana nufin hulɗa)
Human Rights Writers Association of Nigeria (HURIWA) - Ƙungiyar Marubuta Hakikin Dan'adam Ta Najeriya
Hunt - A turance tana nufin farauta. Misali; Samarin na shirin fita farauta yau da daddare. HAU; Farauta (Tana nufin shiga daji don kamo namun daji, don a ci ko a siyar da naman)
Hunturu - Tana nufin lokacin sanyi. Misali; Lokacin hunturu akan kunna wuta domin jin ɗumi. ENG; Cold (A turance tana nufin hunturu)
Hura - Tana nufin fito da iska ta baki. Misali; Tun ɗazu nake hura wutar ta ƙi kamawa. ENG; Blow (A turance tana nufin hura)
Hurry - A turance tana nufin gaggauta. Misali; Ku gaggauta gamawa saboda lokacin tashi ya yi. HAU; Gaggauta (Tana nufin a yi abu da sauri ko hanzari)
Husks of Rice - A turance tana nufin ɓuntu. Misali; Shinkafar da muka siyo cike take da ɓuntu, sai an gyara ta ƙwarai. HAU; Ɓuntu (Tana nufin kwanson da shinkafa ke ciki)
Hut - A turance tana nufin bukka. Misali; Fulani na gina bukka a rugagensu domin su zauna. HAU; Bukka (Tana nufin ƙaramin ɗakin da ake ginawa da busasshiyar ciyawar da ake kira da zana)
1 21 22 23 24