Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Hoto - Tana nufin taswira.
Misali; Idan an gama taron za mu ɗauki hoto saboda tarihi.
ENG; Photograph (A turance tana nufin hoto)
House - A turance tana nufin gida.
Misali; Ya gina ƙaton gida a sabuwar unguwa.
HAU: Gida (Tana nufin mazauni ko gini da ake yi don ba wa kai kariya daga abin cutarwa)
Huce - Tana nufin yin sanyi.
Misali; Abincin da na kawo har ya huce kuna hira.
ENG; Cool Off (A turance tana nufin huce)
Huhu - Tana nufin ɓangaren da ke sarrafa iska a jikin ɗan Adam.
Misali; Shan taba yana illata huhu a wasu lokutan ma har a rasa rai.
ENG; Lungs (A turance tana nufin huhu)
Hujja - Tana nufin dalili.
Misali; Sun yi rashin nasara saboda ba su da ƙwaƙƙwarar hujja a shari'ar.
ENG; Reason (A turance tana nufin hujja)
Hukuamar Bunƙasa Binciken Sararin Samaniya Ta Ƙasa - National Space Research Development Agency (NASRDA)
)
0
Hukuma - Tana nufin gwamnati ko waɗanda ke da ƙarfin iko, da shugabancin al'umma a ƙasa da jiha da ƙananan hukumomi.
Misali; Hukuma ce ke da ikon hukunta wanda ya karya dokar ƙasa.
ENG; Government Body/Authority (A turance tana nufin hukuma)
Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Ƙasa - National Hajj commission of Nigeria (NAHCON)
Hukumar Abinci da Aikin Gona - Food & Agriculture Organization (FAD)
Hukumar Adana Jarin Kamfanoni Ta Ƙasa - National Deposit Insurance Corporation (NDIC)