Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Hollow of tree - A turance tana nufin kogo.
Misali; Karnukan sun shige cikin kogon bishiya a gonar da ke bayan gari.
HAU; Kogo (Tana nufin wani wawakeken rami da ke jikin bishiya kamar ta kuka, tsamiya da sauransu)
Holy war to spread Islam - A turance tana nufin jihadi.
Misali; Sahabbai sun yi jihadi don ɗaukaka addinin musulunci.
HAU; Jihadi (Tana nufin yaƙi don ɗaukaka addinin musulunci)
Hoof - A turance tana nufin kofato.
Misali; Na ga shatin kofato da alama doki ya bi ta nan gurin.
HAU; Kofato (Tana nufin ƙafar dabba kamar saniya ko akuya ko doki)
Hora - Tana nufin ladabtarwa.
Misali; Makarantar suna hora ɗalibai idan sun yi ba daidai ba.
ENG; Discipline (A turance tana nufin hora)
Horarwa - Ba da horo a kan wani ilimi na sana'a ko aiki domin kara gogewa da sabunta fahimta.
Horse - A turance tana nufin doki.
Misali; Almustafa ya hau doki.
HAU; Doki (Tana nufin dabba mai ƙafa huɗu wadda ma'abotra sarauta ke hawa a ƙasar Hausa)
Kishiyarta; Goɗiya
Horse-riding for pleasure - A turance tana nufin kilisa.
Misali; An shirya kilisa a bikin angwancin Abdullahi.
HAU; Kilisa (Tana nufin hawa dokuna don nishaɗi)
Hospitality & Tourism Management Association of Nigeria (HATMAN) - Ƙungiyar Gudanarwa da Tarbar Ƴan yawon Buɗe-Ido To Najeriya
Hot Embers - A turance tana nufin garwashi.
Misali; Ta yi amfani da garwashi wajen gasa cibiyar jaririn.
HAU; Garwashi (Tana nufin diddigar wuta)
Hotel & Personal Services Employers’ Association of Nigeria (HOPESEA) - Ƙungiyar masana'antun Otal da Hidimar Jama'a Ta Najeriya