Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Farilla - Tana nufin dole.
Misali; Yin salla sau biyar a kowacce rana farilla ne akan kowane musulmi.
ENG; Obligatory (A turance tana nufin farilla)
Farka - Tana nufin tashi daga bacci.
Misali; Jaririn ya farka tun ɗazu.
ENG; Wake up (A turance tana nufin Farka)
Farm - A turance tana nufin gona.
Misali; Yana da gona amma ya gaje ta ne a gurin mahaifinsa.
HAU; Gona (Tana nufin fili ko sararin da ake shuka a yi noma)
Farmaki - Tana nufin kai hari ba zato ba tsammani.
Misali; 'Yan ta'adda sun kai farmaki ga jami'an tsaro.
ENG; Sudden Attack (A turance tana nufin farmaki)
Fartanya - Tana nufin wani ƙarfe mai ƙota da ake amfani da shi don yin noma.
Misali; Ado ya saɓa fartanya ya nufi gona.
ENG; Hoe (A turance tana nufin fartanya)
Fasaha - Azancin kirkirar wani abu mai amfani ga rayuwar dan'adam ko dabarar sarrafa tunani domin nishaɗantarwa
Fasahar Bayanai - Azancin sarrafa ko dabarar tsara bayanai
Fasahar Sadarwa - Kusan fusan fasahar bayanai ce.
Fasahar Sana’a - Dabarar sarrafa tunani wajen aiwatar da aikin ko sana'o'in hannu.
Fassara - Tana nufin daga wani harshe zuwa wani harshe.
Misali; Ya fassara littafin daga harshen larabci zuwa harshen Hausa.
ENG; Translation (A turance tana nufin fassara)