Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Faranta - Tana nufin sanya farin ciki. Misali; Matar ta faranta ran mijinta ta hanyar yi masa girki. ENG; Gladden (A turance tana nufin faranta)
Faranti - Tana nufin mazubin abinci. Misali; Ki zuba abincin a faranti don ya huce da wuri. ENG; Plate (A turance tana nufin faranti)
Farar-Hula - Tana nufin wanda ba soja ko mai ɗamara ba. Misali; A Najeriya mulkin farar-hula ake yi. ENG; Civilian (A turance tana nufin farar-hula) Kishiyarta; Soja
Farashi - Tana nufin kuɗin abu. Misali; Ana ta ƙarawa kaya farashi a kasuwa saboda karyewar tattalin arziƙi. ENG; Price (A turance tana nufin farashi)
Farauta - Tana nufin shiga daji don kamo namun daji, don a ci ko a siyar da naman. Misali; Samarin na shirin fita farauta yau da daddare. ENG; Hunt (A turance tana nufin farauta)
Farce - Tana nufin ƙumba. Misali; Salihu yana sana'ar yankan farce. ENG; Fingernail (A turance tana nufin farce)
Farfajiya - Tana nufin filin tsakar gida. Misali; A farfajiyar gidan za a yi taron bikin. ENG; Open space in front of compound (A turance tana nufin farfajiya)
Farfaɗiya - Tana nufin lalurar da ta shafi ƙwaƙwalwa, wadda ke sa mutum ya fita hayyacinsa ya faɗi yana shure-shure. Misali; An buɗe asibitin masu farfaɗiya a garin da muke. ENG; Epilepsy (A turance tana nufin farfaɗiya)
Farfela - Tana nufin fankar da ke jikin mota. Misali; Farfelar motar ta lalace, sai an kai gyara. ENG; Motor Fan (A turance tana nufin farfela)
Farfesu - Tana nufin dafa abu da romo-romo, kamar kaza ko kifi da sauransu. Misali; Tunda ya fara zazzaɓi yake sha'awar farfesu. ENG; Pepper Soup (A turance tana nufin farfesu)
1 2 3 4 5 6 17