Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Fallasa - Tana nufin tona asiri.
Misali; An fallasa abin da suka daɗe suna ƙullawa yau.
ENG;Disclose Secret (A turance tana nufin fallasa)
Falmaran - Tana nufin riga mara hannu da ake ɗorawa a kan mai dogon hannu.
Misali; Falmaran ɗin da yarima ya sa ta yi kyau ƙwarai da gaske.
ENG;Waistcoat (A turance tana nufin falmaran)
Famfara - Tana nufin cirewar da haƙoran yara ke yi kafin na girma ya fito.
Misali; Muntari yana famfara.
ENG; Losing Baby Teeth (A turance tana nufin famfara)
Family - A turance tana nufin iyali.
Misali; Yana kula da iyali yanda ya kamata.
HAU; Iyali (Tana nufin ahali ko kuma uwa da uba da yaransu)
Famous - A turance tana nufin fitacce.
Misali; Alh. Sule fitacce ne a unguwar.
HAU; Fitacce (Tana nufin wanda ya shahara)
Fanka - Tana nufin na'urar da ke ba da iska.
Misali; An kunna fanka a ɗakin saboda yau ana zafi.
ENG: Electric Fan (A turance tana nufin fanka)
Fanke - Tana nufin nau'in abin ci da ake yi da fulawa da sikari da mai da sauransu.
Misali; An yi sadakar fanke a gidan mutuwar.
ENG; Fried cake made of wheat flour (A turance tana nufin fanke)
Fanko - Tana nufin babu komai.
Misali; Gwangwanin fanko ne.
ENG; Empty container (A turance tana nufin fanko)
Fansho - Tana nufin kuɗin da ake ba wa mutum bayan ya kammala shekarun aikinsa.
Misali; Ma'aikata da dama da fansho suke siyan gida.
ENG; Pension (A turance tana nufin fansho)
Faraga - Tana nufin samun dama.
Misali; Mun samu faraga mun yi abubuwan alkhairi da yawa.
ENG; Opportunity (A turance tana nufin faraga)