Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Fahimta - Tana nufin ganewa. Misali; Ɗaliban suna da fahimta ƙwarai da gaske. ENG; Understand (A turance tana nufin fahimta) Kishiyarta; Rashin Fahimta
Fail To Do - A turance tana nufin gaza. Misali; Sakamakon da ya samu ya gaza kai wa yanda za a ɗuake shi a jami'a. HAU; Gaza (Tana nufin kasawa)
Failure - A turance tana nufin kuskure. Misali; Idan mutum ya yi kuskure ya kamata a yi masa afuwa. HAU; Kuskure (Tana nufin yin abu ba daidai ba)
Faith - A turance tana nufin imani. Misali; Yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin rukunan imani. HAU; Imani (Tana nufin yarda, amincewa ko ba da amanna ɗari bisa ɗari)
Fake - Tana nufin samun mafaka. Misali; Lokacin da ruwan ya sakko a shagon na fake. ENG; Take shelter or refuge (A turance tana nufin fake)
Fake - A turance tana nufin jabu. Misali; Madarar jabu ce, idan aka sha tana sa ciwon ciki. HAU; Jabu (Tana nufin abin da ba shi da inganci)
Fako - Tana nufin ɓuya don kai harin ba-zata. Misali; Shi suke fako, yana zuwa suka cafke shi. ENG: Ambush (A turance tana nufin fako)
Faku - Tana nufin mutuwar annabawa ko bayin Allah salihai. Misali; Ba su san annabi ya faku ba. ENG; Death (of prophets or saints) (A turance tana nufin faku)
Falala - Tana nufin alkhairai da dama. Misali; Akwai ɗimbin falala a cikin ambaton Allah. ENG; Abundance, Fortune (A turance tana nufin falala)
Fale-Fale - Tana nufin abu mara nauyi ko kauri. Misali; Yadin da aka ba mu fale-fale ne ba shi da kauri. ENG; Thin and Flimsy (A turance tana nufin fale-fale)
1 2 3 4 17