Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Funeral - A turance tana nufin jana'iza. Misali; Za a yi jana'iza a babban masallacin Juma'a yau. HAU; Jana'iza (Tana nufin sallar da ake yi wa mamaci kafin a kai shi kabari)
Fura - Tana nufin abin sha da ake yi da gero. Misali; An dama mana fura da nono. ENG; Balls made of cooked millet (A turance tana nufin fura)
Fure - Tana nufin tsiro mai ban sha'awa mai ɗauke da launi daban-daban. Misali; An tsinko fure daga lambu. ENG; Flower (A turance tana nufin fure)  
Furfura - Tana nufin farin gashi wanda ke fitowa mutum sakamakon tsufa ko baiwa. Misali; Furfura ta mamaye gashin mahaifina. ENG; Grey Hair (A turance tana nufin furfura)
Furuci - Tana nufin yin magana. Misali; Yana da furuci daddaɗa. ENG; Utterance (A turance tana nufin furuci)
Fusata - Tana nufin tsananin fushi. Misali; Ya fusata sosai har kyarma yake. ENG; So Angry (A turance tana nufin fusata)
Fuska - Tana nufin sashen jiki mai ƙunshe da ido da hanci da baki. Misali; Ta mare shi a fuska hakan ya janyo suka fara faɗa. ENG; Face (A turance tana nufin fuska)
Fyace - Tana nufin fitar da majina daga hanci da ƙarfi. Misali; Tun ɗazu take fyace hanci saboda mura ta kama ta sosai. ENG; Blow One's Nose (A turance tana nufin fyace)
Fyaɗa - Tana nufin duka musamman da tsumagiya. Misali; Ai alamajirin nan ya sha fyaɗa a gurin malaminsu. ENG; Whip, Flog (A turance tana nufin fyaɗa)
Fyaɗe - Tana nufin yin tarayya da mace ta ƙarfi ba da son ranta ba. Misali; Ƙungiyar tana yaƙi da masu fyaɗe a jihar baki ɗaya. ENG; Rape (A turance tana nufin fyaɗe)
1 15 16 17