Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Fusata - Tana nufin tsananin fushi.
Misali; Ya fusata sosai har kyarma yake.
ENG; So Angry (A turance tana nufin fusata)
Fuska - Tana nufin sashen jiki mai ƙunshe da ido da hanci da baki.
Misali; Ta mare shi a fuska hakan ya janyo suka fara faɗa.
ENG; Face (A turance tana nufin fuska)
Fyace - Tana nufin fitar da majina daga hanci da ƙarfi.
Misali; Tun ɗazu take fyace hanci saboda mura ta kama ta sosai.
ENG; Blow One's Nose (A turance tana nufin fyace)
Fyaɗa - Tana nufin duka musamman da tsumagiya.
Misali; Ai alamajirin nan ya sha fyaɗa a gurin malaminsu.
ENG; Whip, Flog (A turance tana nufin fyaɗa)
Fyaɗe - Tana nufin yin tarayya da mace ta ƙarfi ba da son ranta ba.
Misali; Ƙungiyar tana yaƙi da masu fyaɗe a jihar baki ɗaya.
ENG; Rape (A turance tana nufin fyaɗe)