Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Flour - A turance tana nufin gari.
Misali; Mun siyo niƙaƙƙiyar masara za mu yi tuwo.
HAU; Gari (Tana nufin niƙaƙken abu)
Flower - A turance tana nufin fure.
Misali; An tsinko fure daga lambu.
HAU; Fure (Tana nufin tsiro mai ban sha'awa mai ɗauke da launi daban-daban)
Food & Agriculture Organization (FAO) - Hukumar Abinci da Aikin Gona
Food made of grinded corn, moringa, onion etc - A turance tana nufin dambu.
Misali; Dambu za a yi a gidan sunan Rakiya.
HAU; Dambu (Tana nufin abincin da ake yi da tsakin masara da zogale da albasa da sauransu)
Food/Meal - A turance yana nufin abinci.
Misali; Muna cin abinci sau uku a rana.
HAU; Abinci (Yana nufin duk abinda za a ci ya kawar da yunwa)
Fool - A turance tana nufin dolo.
Misali; Yaron dolo ne, ya samu matsalar ne tun daga haihuwa.
HAU; Dolo (Tana nufin wanda yake da ƙarancin hankali da fahimta)
Football Writers Association (FWA) - Ƙungiyar Marubuta Wasan Ƙwallon Ƙafa
Fore-arm - A turance tana nufin damtse.
Misali; Masu manyan damtse yawancin su ƙarfafa ne.
HAU; Damtse (Tana nufin gaɓar da take saman hannu)
Forestry Research Institute of Nigeria (FRIN) - Cibiyar Nazarin Gandun Daji Ta Najeriya
Forum - Ƙungiya, Kadaura