Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Casa - Tana nufin cire tsaba daga cikin kwansonta, kamar shinkafa da gero da sauransu.
Misali; Sai an casa shinkafar sannan za a dafa.
ENG; Thresh Grain (A turance tana nufin casa)
Cat - A turance tana nufin mage.
Misali; Gidansu Hanan suna da ƙaton kule.
HAU; Kule (Tana nufin mage)
Catch - A turance tana nufin kama.
Misali; Jami'an tsaro sun kama masu lefi da yawa a wannan makon.
HAU; Kama (Tana nufin riƙe abu da hannu)
Catch Something - A turance tana nufin cafe.
Misali; Mai tsaron ragar ya cafe ƙwallon da aka bugo masa.
HAU; Cafe (Tana nufin kama abu da sauri)
Cattle Tax - A turance tana nufin jangali.
Misali; Malam Modibbo ya biya jangali da wuri wannan karon.
HAU; Jangali (Tana nufin kuɗin harajin da ake biyawa shanu)
Cause - A turance tana nufin haddasa.
Misali; Zuwanta a makare shi ya haddasa ta rasa gurin zama.
HAU; Haddasa (Tana nufin sila ko zama dalilin faruwar wani abu)
Caɓa - Tana nufin yin ado da yawa.
Misali; Amaryar ta caɓa ado sosai.
ENG; Make Slushy (A turance tana nufin caɓa)
Caɓi - Tana nufin jiƙaƙƙiyar ƙasa.
Misali; Ka yi hankali da caɓi a hanyar saboda jiya an kwana ana ruwa.
ENG; Mud (A turance tana nufin caɓi)
Celebration - A turance tana nufin biki.
Misali; Zan je biki gobe da yamma, ƙanwata ce za ta yi aure.
HAU; Biki (Tana nufin tara mutane su ci su sha saboda taya murnar wani abin farin ciki da ya samu)
Cement Block - A turance tana nufin bulo.
Misali; Gidan da aka gina da bulon siminti ya fi ƙarko.
HAU; Bulo (Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin gini)