Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Crush - A turance tana nufin dagargaza.
Misali; Matasan sun dagargaza gilasan ginin yayin faɗace-faɗacensu.
HAU; Dagargaza (Tana nufin farfasa abu a yi masa rugu-rugu)
Crying - A turance tana nufin kuka.
Misali; Safiya ta sha kuka lokacin da mahaifinta ya rasu.
HAU; Kuka (Tana nufin zubar hawaye daga idanu sakamakon murna ko ɓacin rai)
Cudgel - A turance tana nufin kulki.
Misali; Ɗan dokar na riƙe da kulki lokacin da suka je kama ɓarayin.
HAU; Kulki (Tana nufin gajeren sanda mai kauri wanda 'yan doka suke riƙewa)
Cuku-cuku - Tana nufin yin 'yan dabaru don samun abin da ake so.
Misali; Ya yi cuku-cuku har ya samun aikin.
ENG; Obtaining things through devious (A turance tana nufin cuku-cuku)
Curriculum Organization of Nigeria (CON) - Ƙungiyar matsara manhaja ta Najeriya
Cushion - A turance tana nufin kushin.
Misali; Hedimasta yana zaune a kan kushin ɗin ofishinsa a lokacin da muka kai masa ziyara.
HAU; Kushin (Tana nufin kujerar bature)
Cut Off - A turance tana nufin katse.
Misali; Idan aka katse min bacci ciwon kai yake sa ni.
HAU; Katse (Tana nufin yankewa ko tsayar da abu)
Cut Short - A turance tana nufin guntule.
Misali; A musulunci hukuncin sata shi ne guntule hannu.
HAU; Guntule (Tana nufin yanke wani sashi)
Cuta - Tana nufin rashin lafiya.
Misali; Wata sabuwar cuta ta ɓullo mai suna korona.
ENG; Illness (A turance tana nufin cuta)
Cuɗanya - Tana nufin mu'amala da mutane.
Misali; Na yi cudanya da mutane da dama da na je Turai.
ENG; Mingling With Others (A turance tana nufin cuɗanya)