Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Canine Tooth - A turance tana nufin fiƙa.
Misali; Yaron ya fara fiƙa.
HAU; Fiƙa (Tana nufin haƙoran gaba)
Canja - Tana nufin sake wani abu da wani.
Misali; An canja lokacin jarrabawar daga ƙarfe ɗaya zuwa ƙarfe biyu na rana.
ENG; Change (A turance tana nufin canja)
Cankacakare - Tana nufin ƙarewar abu ƙarƙaf.
Misali; Kayan marmarin sun zama cankacakare.
ENG; Running short of something (A turance tana nufin cankacakare)
Cap - A turance tana nufin hula.
Misali; Ya sanya hula zanna bukar 'yar Maiduguri.
HAU; Hula (Tana nufin nau'in sutura da ake sa wa a kai)
Cara - Tana nufin kukan da zakara yake yi musamman da asuba.
Misali; Tun da zakara ya yi cara na farka.
ENG; Cock Crow (A turance tana nufin cara)
Carabke - Tana nufin wasa da ake yi da dutse, inda ake wurga dutse sama a cafe shi da hannu.
Misali; 'Yan matan suna 'yar carabke a ƙofar gida.
ENG; Game of tossing and catching stones on hands (A turance tana nufin carabke)
Caring For - A turance tana nufin gata.
Misali; 'Ya'yan Alhaji Jibrin na da gata saboda ya sa su a makaranta mai tsada.
HAU; Gata (Tana nufin samun duk abinda ake buƙata na rayuwa)
Carkwai - Tana nufin zaƙi sosai.
Misali; Raken yana da zaƙi carkwai.
ENG; Very Sweet (A turance tana nufin carkwai)
Carrying load for payment - A turance tana nufin dako.
Misali; Ƙungiyar masu dako sun koka kan ƙarancin biyansu da mutane ke yi.
HAU; Dako (Tana nufin ɗaukarwa mutum kaya a kai masa inda yake so, ya biya)
Cartilage - A turance tana nufin guringuntsi.
Misali; Guringuntsi na da daɗi musamman a miyar taushe.
HAU; Guringuntsi (Tana nufin ƙashi mai laushi da ke jikin ɗan Adam da dabba)