Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Consumer Protection Council (CPC) - Hukumar kare Haƙƙin matsayi (Mamori)
Cook - A turance tana nufin dafa
Misali; Sai da aka dafa abincin aka yi sadakar da shi.
HAU; Dafa (Tana nufin sa abu a cikin tukunya a zuba ruwa a ɗora a wuta har ya yi laushi)
Copyright Society of Nigeria (CSN) - Ƙungiyar haƙƙin mallaka ta Nijeriya
Cornstalk Fence - A turance tana nufin danga.
Misali; Baba yana waje jikin danga tare da amininsa suna magana.
HAU; Danga (Tana nufin kewaye gida da karan masara)
Corporation - Kamfani, Hukuma
Corps - Runduna, Hukuma
Correctly - A turance tana nufin dai-dai.
Misali; Wanda ya yi aikinsa dai-dai zai samu sakamako da kyautatawa.
HAU; Dai-dai (Tana nufin yadda ya dace)
Cotton - A turance tana nufin auduga.
Misali; Akwai gonakin auduga da yawa a garinmu.
HAU; Auduga (Tana nufin tsiro da ake shukawa a gona, ana amfani da ita wajen yin zare da tufafi da sauransu)
Council - Hukuma, Majalisa
Council for the Regulation of Engineering in Nigeria (CREN) - Hukumar inganta ayyukan injiniyoyi ta Najeriya