Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ciniyar Ƙwararrun AKantoci Ta Najeriya - Instutite Of Chartered Acoountants Of Nigeria (ICAN)
Cinnaka - Tana nufin ɗan ƙaramin baƙin ƙwaro, yana cizo mai zafi. Misali; Idan cinnaka ya ciji mutum gurin har ɗan kumbura yake. ENG; Small black biting ant (A turance tana nufin cinnaka)
Circle - A turance tana nufin da'ira. Misali; Yara sun yi da'ira suna wasa. HAU; Da'ira (Tana nufin zagayayye)
Ciroma - Tana nufin sarautar da ake ba wa ɗan sarki. Misali; An naɗa yarima a matsayin ciroma jiya bayan la'asar. ENG; A traditional title usually held by son of an emir (A turance tana nufin ciroma)
Citta - Tana nufin ɗaya daga cikin sinadaran abinci mai inganci ga lafiya, tana da yaji, kuma akwai ɗanya akwai busasshiya. Misali; An zuba wadatacciyar citta a yajin. ENG; Ginger (A turance tana nufin citta)
Civil Service Commission (CSC) - Hukumar ma'aikatan gwamnti
Civil Service Commission (CSC) - Hukumar ma'aikatan Gwamnati
Civil Society Organizations (CSO) - Gamayyar ƙungiyoyin sa-kai
Civilian Joint Task Force (CJTF) - Rundunar mayaƙan sa-kai
Civilian Joint Task Force (CJTF) - Rundunar mayakan sa-kai
1 20 21 22 23 24 26