Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Cibiyar Ƙwararrun Masana Tattali Ta Nijeriya - Instutite Of Chartered Economists Of Nigeria (ICEN)
Cibiyar Ƙwararrun Masana Ɗaukar Ma’aikata - Instutite Of Professional Recruitment Consultants (IPRC)
Cibiyar Ƙwararrun Matsara Birane Ta Najeriya - Nigerian Instutite Of Town Planners (NITP)
Cicciɓa - Tana nufin ɗaukar abu mai nauyi. Misali; Buhun simintin za mu cicciɓa mu kai saman benen. ENG: Lift and carry something heavy (a turance tana nufin cicciɓa)
Cida - Tana nufin rugugin tsawa yayin da ake ruwan sama. Misali; Ruwa ake da cida tun da safe har ga shi yamma ta yi. ENG; Thunder Rumbling (A turance tana nufin cida)
Cifjoji - Tana nufin alƙalin alƙalai. Misali; Ai wanda ya yi mana shari'ar cifjoji ne, kuma ya kwatanta adalci. ENG; Chief Judge (A turance tana nufin cifjoji)
Ciko - Tana nufin ƙara biyan kuɗi.  Misali; Da na siyo kayan sai da na yi ciko, saboda sun tashi. ENG:Balance/ Outstanding (A turance tana nufin ciko)
Cimaka - Abincin da ake ci domin rayuwa.
Cincirindo - Tana nufin taruwar mutane da yawa. Misali; Mutane sun yi cincirindo a ƙofar gidan sarki. ENG;Dense Crowd (A turance tana nufin cincirindo)
Cindo - Tana nufin wanda aka haifa da yatsu shida. Misali; Jaririn da Latana ta haifa yana da cindo. ENG; Person with sixth finger (A turance tana nufin cindo)
1 19 20 21 22 23 26