Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Cakwaikwaiwa - Tana nufin tsuntsuwa ma'abociyar rera waƙa.
Misali; Na ji cakwaikwaiwa na waƙa a kan bishiya a makarantar mu.
ENG; Sterling (A turance tana nufin cakwaikwaiwa)
Calabash Mender - A turance tana nufin gyartai.
Misali; Babansa gyartai ne tun shekarun baya.
HAU; Gyartai (Tana nufin mai gyaran ƙwarya)
Calamity - A turance yana nufin bala'i.
Misali; Ƙasashen yamma na cikin bala'i saboda afkuwar yaƙe-yaƙe.
HAU; Bala'i (Tana nufin faruwar abubuwan tashin hankali da firgici)
Calendar - A turance tana nufin kalanda.
Misali; Sabuwar kalandar muslunci ta fito.
HAU; Kalanda (Tana nufin jadawalin da ke ƙunshe da watanni goma sha biyu na shekara)
Cali - Tana nufin jaka mai raga-raga.
Misali; A zuba tumaturan a cikin cali saboda kar ya lalace.
ENG; Net Bag (A turance tana nufin cali)
Camfi - Tana nufin yadda da maganganu marasa tushe.
Misali; Mutanen da sun yadda da camfi sosai.
ENG; Superstition (A turance tana nufin camfi)
Can - Tana nufin nesa da inda ake.
Misali; Na ajiye butar a can.
ENG; Over there (A turance tana nufin can)
Canary - A turance tana nufin kanari.
Misali; Tun asuba nake jin kukan kanari a kan bishiyar gidan nan.
HAU; Kanari (Tana nufin wani nau'in tsuntsu ma'abocin rera waƙa)
Cancak - Tana nufin ɗungurungum, wato a ɗauke abu gaba ɗayansa.
Misali; Ta ɗauke jakar cancak daga kan teburin.
ENG; Completely Gone (A turance tana nufin cancak)
Cancanta - Tana nufin dacewa.
Misali; Malamin ya cancanta a ba shi lambar yabo, saboda ƙokarinsa.
ENG; Deserve (A turance tana nufin cancanta)