Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Cheeks - A turance tana nufin kumatu.
Misali; Fauziya ta shafa hoda a kumatu.
HAU; Kumatu (Tana nufin jam'in kunci wato gefen fuska na hagu ko na dama)
Chemical Society of Nigeria (CSN) - Ƙungiyar masana sinadarai ta Najeriya
Chemical Society of Nigeria (CSN) - Ƙungiyar masana sinadarai ta Najeriya
Chest -
A turance tana nufin ƙirji.
Misali: Ya ji ciwo a ƙirji bayan ya yi gudu mai tsawo.
HAU: Ƙirji (Tana nufin sashen jikin mutum da ke tsakanin wuya da ciki)
Chewing Stick - A turance yana nufin asawaki.
Misali; Na tarar yana asawaki da na je gidan.
HAU; Asawaki (Itace ne da ake goge haƙora da shi)
Chicken/Hen - A turance tana nufin kaji.
Misali; An soya kaji za a yi mana miya da su.
HAU; Kaji (Tana nufin jam'in kaza)
Chickenpox - A turance tana nufin ƙarambau.
Misali; Yaron ya kamu da ƙarambau, don haka ba ya zuwa makaranta har sai ya warke.
HAU; Ƙarambau (Tana nufin cutar fata da ke sa ƙuraje ƙanana masu ruwa su fito a jiki, musamman ga yara)
China Radio International (CRI) - Gidan Rediyon caina /sin
Choke - A turance tana nufin ƙware.
Misali: Yaron ya ƙware da abinci.
HAU: Ƙware (Tana nufin shaƙewa ko toshewar maƙogwaro ta yadda numfashi ko haɗiyar abinci zai yi wuya)
Christian - A turance tana nufin banasare.
Misali; Wani banasare ya tare a yankin nan.
HAU; Banasare (Tana nufin mai bin addinin kiristanci)