Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Worship - A turance tana nufin bauta.
Misali; Musulmai sun yarda da Allah shi ne kaɗai abin bauta.
HAU; Bauta (Tana nufin sadaukarwa da biyayya ga abinda mutum ya yarda da shi)
Worth, Value - A turance tana nufin daraja.
Misali; Zinare na da daraja a halin yanzu.
HAU; Daraja (Tana nufin muhimmanci ko tsada)
Wrestling - A turance tana nufin kokawa.
Misali; Su Lado sun tafi kallon kokawa a dandali.
HAU; Kokawa (Tana nufin ɗaya daga cikin wasannin gargajiya, inda maza biyu ke doke-doke a tsakaninsu har a kayar da ɗaya)