Terms Dictionary

Halal - Tana nufin duk abin da addini ya ba da damar a yi. Misali; Cin naman shanu halal ne a musulunci. ENG; Any Lawful Act (A turance tana nufin halal) Kishiyarta; Haram
Halarta - Tana nufin samun damar zuwa gurin da aka gayyaci mutum. Misali; Taron da aka gabatar a makon da ya gabata, mutane da dama sun halarta. ENG; Attend (A turance tana nufin halarta)
Hali - Tana nufin ɗabi'a. Misali; Ya kasance mai kyakkyawan hali shi yasa ake son shi. ENG; Character (A turance tana nufin hali)
Halitta - Tana nufin ƙirƙirarren abu. Misali; Allah shi ne ya ƙagi Annabi Muhammad (SAW) ya sa ya zamo shugaban halitta baki ɗaya. ENG; Creature (A turance tana nufin halitta)
Hallara - Tana nufin zuwa ko bayyana ko samun damar halarta. Misali; Mutane sun hallara, ya kamata a fara taron. ENG; Appear/Arrive (A turance tana nufin hallara)
Hamada - Tana nufin guri mai cike da rairayi da duwatsu wanda dabbobi da tsirrai  ba sa sakewa. Misali; Ƙasar da ke maƙotaka da mu cike take da hamada ENG; Desert (A turance tana nufin hamada)
Hamayya - Tana nufin kishi ko takun saƙa. Misali; Abokan hamayya ne su a siyasa shi yasa ba sa ga maciji. ENG; Rivalry/Opponent (A turance tana nufin hamayya)
Hambuɗa - Tana nufin ɗiban abu a watsa a baki. Misali; Madara ta hambuɗa a baki ta gudu. ENG; Throw powdered or ground thing into the mouth (A turance tana nufin hambuɗa)
Hamma - Tana nufin fitar da iska ta hanyar buɗe baki wanda jin yunwa ko bacci ke sa wa. Misali; Tun ɗazu nake hamma saboda yunwa nake ji matuƙa. ENG; Yawning (A turance tana nufin hamma)
Hammata - Tana nufin gaɓar ƙarƙashin hannu. MIsali; An ce goga alimun a hammata yana hana warin jiki. ENG; Armpit (A turance tana nufin hammata)
1 129 130 131 132 133 300