Terms Dictionary

Hagu - Tana nufin ɓarin hagu a jikin ɗan Adam, idan aka kalli mutum daga sama zuwa ƙasa, ɓari ɗaya shi ne hagu ɗayan kuma dama. Misali; Da hannun hagu yake rubutu. ENG; Left (A turance tana nufin hagu) Kishiyarta; Dama
Haila - Tana nufin jinin da mata ke fitarwa a kowanne wata. Misali; Matan da ke haila ba sa shiga masallaci. ENG; Menstruation (A turance tana nufin haila)
Hair - A turance tana nufin gashi. Misali; Mata sun fi maza yawan gashi. HAU; Gashi (Tana nufin tsiron da ke fitowa a saman fatar ɗan Adam ko dabba)
Hajijiya - Tana nufin jujjuyawa. Misali; Maganin da na sha ya sa ni jin hajijiya. ENG; Dizziness (A turance tana nufin hajijiya)
Hajj - A turance tana nufin hajji. Misali; Maniyyata aikin hajji na zuwa bita a kowane mako don sanin yanda za su gudanar da aikin. HAU; Hajji (Tana nufin ɗaya daga cikin shikashikan musulunci)
Hajji - Tana nufin ɗaya daga cikin shikashikan musulunci. Misali; Maniyyata aikin hajji na zuwa bita a kowane mako don sanin yanda za su gudanar da aikin. ENG; Hajj (A turance tana nufin hajji)
Haki - Tana nufin ciyawa. Misali; Na samo hakin da zan yi amfani da shi don yin maganin. ENG; Grass (A turance tana nufin ciyawa)
Haki - Tana nufin yin numfashi sama-sama da sauri. Misali; Gudun da na yi ya sa ni haki. ENG; Panting, Gasping (A turance tana nufin haki)
Hakimi - Tana nufin muƙamin sarauta na shugaban lardi. Misali; Hakimi aka naɗa shi a shekarar da ta gabata. ENG; District Head (A turance tana nufin hakimi)
Hakiya - Tana nufin ciwon da ke fitowa a cikin ido. Misali; Hakiya ce ta fito masa a ido. ENG; Leucoma (A turance tana nufin hakiya)
1 128 129 130 131 132 300