Idan Mutum Ya Samu Kanshi Ko Yayi Tafiya Zuwa Inda Rana Take Kaiwa Wata Shida Ko Kasa Da Haka, Ba Tare Da Dare Ya Shigo Ba, Ko Kuma Dare Yake Yin Wata Shida Ko Ƙasa Da Haka, Ba Tare Da Rana Ta Hudo Ba, Yaya Zaiyi Da Azumi?

0
325

Amsa: Idan mutum ya samu kansa a irin waɗannan ƙasashe da ake dare ko rana na tsahon lokaci, zaiyi amfani ne da (time zone) wato ƙasashen da lokutansu yazo ɗaya. Amma su suna samun shigowar rana da dare, sai ya ɗauki azumi lokacin da suke ɗauka, ya sha ruwa lokacin da suke sha.

Haka kuma zai iya amfani da ƙasar da take kusa dasu, wacce bata da irin wannan yanayin; ya kalli awowin da suke yin azumin Ramadan na wannan shekarar. Misali suna yin azumin awa 11 ko 12 arana, to shima haka zaiyi; kuma ta fuskar ganin watan Ramadan ma ko Shawwal, haka zaiyi.

Hujja: (Daarul Ifata’i Almisiriya).

Domin karanta cikakken bayani akan Idan Mutum Zaiyi Tafiya, Koda A Jirgi Ne, Zai Ajiye Azumi? danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Shin Mai Cikin Da Ta Ajiye Azumi Ciyarwa Za Tayi, Ko Bari Za Tayi Tarama Bayan Ta Haihu? danna nan.

Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

labarin da ya wuceIdan Ana Bina Bashin Azumin Ramadan 5 Ko 7, Har Wani Ramadan Ɗin Ya Sake Zuwa, Zan Iya Ciyar Da Mutum 5 Ɗin Ko 7 Arana Ɗaya Lokaci Ɗaya?
Labarin na GabaIdan Mutum Zaiyi Tafiya, Koda A Jirgi Ne, Zai Ajiye Azumi?
Lawan Bello
Abu muzaffar Malami ne masanin ilimin zamani da na addini bisa tsaren Ƙur'ani da tafarkin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, mai hangen nisa a addini da kuma alummma, shugaban Abu Muzaffar foundation.