Shin Mai Cikin Da Ta Ajiye Azumi Ciyarwa Za Tayi, Ko Bari Za Tayi Tarama Bayan Ta Haihu?

0
157

Amsa: Mai ciki da mai shayarwa, malaman da suka ɗauke su a matsayin marasa lafiya na ɗan lokaci sunce; “Zata rama bayan sallah”.

Kamar Al-imamu Maalik, malaman da suka ɗaukesu a matsayin marasa lafiya, sunce; “Su ciyar kuma su rama bayan sallah”. Kamar Al-imamu Shafi’i, malaman da suka ɗauke su a matsayin waɗanda baza su iya azumi ba; bisa uzuri na rauni kamar uzurin tsofaffi sunce; “Baza su rama ba, ciyarwa kawai za su yi cikin azumi”

Kamar Ibnu Abass, Ibnu Umar.

Hujja: (Fatawar Ibnu Abbas da Ibnu Imar) littafi: Bidaayatul Mujtahid wa Nihaayatul Muqtasid, Ibnu Rushdin.

Domin karanta cikakken bayani akan Idan Alfijir Ya Fito, Kuma Da Janaba A Jikina Cikin Ramadan, Yaya Azumina? danna nan.

Domin karanta cikakken bayani akan Shin Idan Na Kwanta Barci, Sai Na Wayi Gari Janaba Ta Same Ni; Ta Hanyar Mafarki Ko Kwanciyar Aure, Zan Iya Ɗaukar Azumi, Ko Sai Nayi Wanka? danna nan.

Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

labarin da ya wuceShin Ya Hallata Mai Ciki Ta Ɗauki Azumi?
Labarin na GabaIdan Alfijir Ya Fito, Kuma Da Janaba A Jikina Cikin Ramadan, Yaya Azumina?
Abu muzaffar Malami ne masanin ilimin zamani da na addini bisa tsaren Ƙur'ani da tafarkin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, mai hangen nisa a addini da kuma alummma, shugaban Abu Muzaffar foundation.