Amsa: Ita tafiya komai sauƙinta, sunanta tafiya, idan mutum ya ajiye azumi, ya aikata sunna; idan kuma yayi azuminsa, babu laifi, azuminsa yayi. Saidai idan yin azumin, zai jefa shi cikin asara, ta rai ko lafiya ko hankali, to anan, wajibi ne ya ajiye azumin, sai ya rama bayan sallah.
Hujja: “Shugaban halitta yasa ankawo masa ruwa a kofi, ya ɗaga sama, yadda kowa zai gani, sannan ya sha akan hanyarsu ta tafiya, akace masa, wasu basu ajiye azumin ba, yace sune suka zaɓar wa kansu shan wahala”.
Marawaici Jabir Ibn Abdullah, littafi Sahihu Muslim.
Domin karanta cikakken bayani akan Mutum Zai Iya Ramawa Iyayensa Azumin Ramadan? danna nan.
Domin karanta cikakken bayani akan Idan Alfijir Ya Fito, Kuma Da Janaba A Jikina Cikin Ramadan, Yaya Azumina? danna nan.
Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.