Category: WikiHausa

Yadda ake amfani da WikiHausa

  • Asalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani

    Asalin Tsibbu A Tsangayun Alƙur’ani

    Tsibbu ararriyar kalma ce daga harshen Larabci “Ɗibbu” ma’ana magani. Kafin zuwan Musulunci, babu wata hanya ta magani sai bori da bokanci.

    Koda Musulunci ya bayyana, sai ya tsawatar ga barin abubuwan da suka ci karo da tauhidi da imani da Allah Maɗaukaki da Manzonsa (Sallallahu Alaihi Wa Sallam). Tsibbu dai ya samo asali ne daga irin yadda malamai ke horon iyaye da almajirai game da yin sadaka a matakin karatu daban-daban. A riyawar su, rashin yin hakan kan jawo

    wa almajirai haukacewa.

    Kasuwar tsibbu ta buɗe cikin tsangayu a daidai lokacin da aka fara hulɗa tsakanin malamai da ‘yan kasuwa da kuma masu mulki. Ma’ana, a da magungunan tsibbu waɗanda ba su wuce ayoyin Alƙur’ani ba, sun taiƙaitu tsakanin ahalin tsangaya.

    Musamman ma don kafin tilawa, da fahmi da gyaran hadda. Sai kuma ɓangaren mugunta, wadda ta shafi ɓata karatun wani, ɗaure karatun wani, ɓatar da kundi da dai sauran su.

    Farkon fitar tsibbu daga da’irar tsangaya kamar yadda (Jibrin, 1987) ke bayyanawa, ya faro ne daga ba wa mutane taimakon tsaron ƙasa da masu mulki. Sai kuma ba wa ‘yan kasuwa da fatake taimakon samun jama’a da tsari daga ‘yan fashi da ɓarayi. Su kuwa masu sana’o’i aka fara ba su taimakon albarkar hannu da tagomashi da tsaraka.

    A farko farkon bayyanar tsibbu, makaranta kan hausantar da nassin Alƙur’ani (Bunza, 1990) daidai da buƙatar da ake so a cimma, ba tare da an san fassarar ta ba. Misali:

    1. Laƙanin ƙarfin mazakuta: Sai a rubuta “Izazul” saboda kalmar “zul” ta yi kama da ƙarfin mazakuta a Hausance.
    2. Lakanin sauƙin haihuwa ko naƙuda: sai a rubuta “yakhriju min sul” don dai jinjiri ya fito sul.
    3. Laƙanin samun kasuwa: a rubuta “tabbat yada” ya zuwa “sayas” ma’ana za a sayar. Ko a yi wuridin “fala talumuni” musamman wurin Fulani, saboda kalmar “Lumo” na nufin kasuwa da Fulatanci.
    4. Laƙanin ga ‘yan dambe:sai a rubuta “kalla iza dukkatil ardi “dakkan dakka” saboda ya yi kama da sautin duka.
    5. Laƙanin damun fura:sai a rubuta “maadamuu fiha” saboda Kalmar “damu” tayi daidai da damun fura.
    A lokacin da ilmi ya ƙara bayyana sai masu tsibbu suka fara duban ma’anar aya ana haɗa ta da buƙatar da ta dace da ita kamar:
    – Maganin soyayya – “wa’alƙaitu alaika muhabbatan”
    – Maganiin makanta ko ciwon ido – “fabasarukal yauma hadid”
    – Maganin kafe mace – “maakisina fihi abada” Da sauransu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Narkewar Tsibbu Cikin Bokanci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Tsarin Tsangayun Alƙur’ani A Arewacin Najeriya Tarihin Su Da Zamantakewar Su Da Hanyoyin Raya Su; wanda Dr. Sunusi Iguda Ƙ/Nasarawa ya wallafa shi; domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Takaiceccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko

    Takaiceccen Tarihin Rayuwar Dr. Yahaya Tanko

    Rayuwar Yahaya Tanko A Taƙaice

    Wanda Aka Gabatar A Taron Walima Wanda Majalissar Mata Ta Shirya A Ɗakin Taro Na Tsangayar Kimiyya Ta Jami’ar Bayero Ranar Lahadi 27 Ga J/Sani=26 Ga Maris 2017

    Ƙuruciya da Aure:

    • An haife shi unguwar Bakinruwa ƙaramar hukumar Dala a 1951
    • Yayi ƙuruciyarsa rabi a Bakinruwa rabi a unguwar kakanisa yakasai, bayan rasuwar mahaifinsa.
    • Ya yi aure a shekarar 1974

    Karatu Da Tarbiyya:

    • Ya fara samun tarbiyya a hannun mahaifansa.
    • Yana da kimanin shekar biyar mahaifinsa ya sa shi a makarantar allo ta Alhaji Malam Isa a unguwar ‘yar kasuwa kan titin kasuwar kurmi zuwa goron dutse.
    • Karatun ƙawa’idi a wurin Malam Abdu na unguwar ‘yan muruci.
    • Makarantar dare ta Islamiya ta Malam Baba Baƙinruwa.
    • Makarantar Ulumiddini ta Alhaji Sunisi Ɗantata a shekarar 1960, a wannan lokacin yana da kimanin shekara takwas ko tara a duniya.
    • Makarantar “Judicial School ta Shahunci 1964-1968. A sannan yana da shekara sha 12 a duniya.
    • Yayi wta tafiya ta ziyarar ‘yar uwarshi a mina (Jihar Neja) a 1970.

    Koyon Sana’a Da Kasuwanci:

    • a sanda yake uruciya mahaifiyarsa takan dora masa tallan acma/acamo. A sanda yake “Judicial” mahaifinsa yana koya masa sana’ar gidansu, watau dinkin keke. Bayan rasuwarsa a shekarar 1967, daga shekarar 1968 zuwa shekarar 1970 kwunsa ya sa shi harkar kasuwanci. Ya yi kasuwanci a wani kanti cikin asibitin Murtala. Ya yi kasuwanci a wani kanti a Galadima Road Sabongaroi. Ya kuma yi ciniki a wani dan kanti na katako a cikin lungun kurna a unguwar yakasai. A sanda yake makarantar SAS,  mahaifiyarsa takan dora masa dubulan/cincin mai nama daga Bakin ruwa ya kai kantin asibiti.

    KARATU:

    Ya fara karatun Alkur’ani a makarantar Alhaji Malam Isa, unguwar ‘yar Kasuwa.

    Ya fara karatun Ilimin (Ahlari/Kawa’idi) a wurin M Abdu a Unguwar ‘Yan muruci.

    Ya fara karatun Islamiyya a                       a unguwar Koki 1960.

    An sa shi a makarantar K Shari’ah ta shahunci 1964-1968.

    Yayi karatun Ilimi na a zure a hanin kakansa Malam Abdur Razak, alkalin Ringim.

    Ya sauke AlQur’ani a makarantar malam Abdu mai ‘yan makaranta wadda take a Yakasdai.

    Ya je Makarantar Nazarin Harshen Larabci (SAS) a 1971.

    Yaje Abdullahi Bayero College (Diploma in Arabic Hausa and Islamic Studies) 1975-1978.

    Digirin farkao a Bayero University (Hausa Islamic Studies) 1980-1983.

    Digiri na biyu a Bayero University (Isalmic Sturdies) 1988-1981.

    Kwas na horar da Limamai a jami’ar Al Azhar (Nov-jan) 1994-1995.

    Digiri na uku a Bayero University ( Islamic Studies)  2011.

    Koyarwa A Makarantun Gwamnati:

    • ya fara koyarwa a makarantar firamare ta Dwanau,1974-1975.
    • Koyarwa a makarantar koyon harshen Larabci (SAS) , 1978-9179.
    • Ma’aikatar Ilimi ta jihar Kano ta bayar dashi aro domin koyar da IRK a “Federal Governent Coliege Kano” 1979-1980.(sai ya tafi kartu)
    • Koyarwa a makarantar mata ta Arabiyya Ɗanbatta 1884-1985
    • Koyarwa a Gumel A.T.C (Kano State Higher Institute of Education) 1985-1960
    • Koyarwa a “College of  Edukation Kumbotso”, wadda a yanzu ake kira “Sa’adatu Rimi College” 1987-1992.
    • Koyarwa a “Aminu School Of Islamic Legal Studies” Kano State polytechnic 1999-Febuary 2015.

    Koyarwa A Makarantun Islamiyyah:

    • Ya koyar a makarantar Islamiyya ta Yola da yamma.
    • Ya koyar a makarantar Islamiyya ta dare a unguwar  Mai Aduwa.
    • Ya buɗe makarantar Iasamiya ta dare a idansa B/R
    • Ya koyar a makarantar koyar da matan aure ta dare ta Gumel
    • Ya koyar  a makarantar koyar da matan aure ta ƙungiyar  Da’awa da yamma.
    • Ya koyar a makarantar koyar da matan are  ta Ƙungiyar Huɗaibiyya

    Limanci

    • Ya fara yin na’ibin limanci Juma’a  tsohuwar Jami’ar Bayero tun 1991,
    • An naɗa shi na’ibin limanci Juma’a a masallacin Umar bin Khaɗɗab a shekarar 1998
    • Yayi limacnci a masallacin Muntada, wanda aka fi sani da Masallacin VC na sabuwar Jami’atun 1998.
    • Yana limanci a masallacin Nana A’ishah FCE

    Gudanar Da Gwamnati:

    • A sanda yake koyarwa a BYK ya nemi hutu daga Jami’a ya yi aiki a Hukumar Zakka ta Jihar Kano, a matsayin kwamishina, ya kuma yi aiki a Hukumar Shari’a a matsayin babban darakta 2004-2011.

    Darussa A Masallatai:

    • Masallacin Juma’a na Jami’ar Bayero tsohuwa.
    • Masallacin Jami’ar bayero sabuwa.
    • Masallacin Juma’a na Umar bin Khaɗɗab.
    • Masallacin Nana A’isha na kan titin FCE Ƙofar Ɗakawuya.
    • Masallacin Khalid BIN Alwalid na cikin Unguwar Ɗakawuya

    Littafai Da Maƙaloli:

    A. Liittafai:

    1. Kayyaɗe Iyali Da Matsayinsu A Musulunci                          1988
    2. Matsayin Kuɗin Ruwa Da Bashin Banki A Msulunci          1993
    3. Zaman Aure A Musulunci                                                       1992
    4. Tarbiyar Yara A Musulunci                                                     1994
    5. Matan Annabi        “Wives of the Prophet                           1994
    6. Bankin Musulinci Wanda Babu Ruwa                                  1994
    7. Addu’o’in Annabi A Wni Da Dare                                         1995
    8. Shin Bankin Yan Kasuwa Ne?                                                 1995
    9. NASIHA Ga Musulmai A Kan Gardamar Watan Azumi     1997
    10. Matan Sahabbai Na Ɗaya                                                       1997
    11. Kasuwanci A Musulunci                                                          1997
    12. Tsaraba Ga Mawadata Da Mabuƙata                                  2004
    13. Muhimmacin Lokaci Ga Musulmi                                         2005
    14. Siyasa A Musulinci “Politics In Islam”
    15. A Brief abaut Busuness in Islamic Banking, on the Basic of Shari’ah  and  Jurisprodence.  2011
    16. Darul Umma For Publishing, Kano.
    17. (in Arabic)                                                                           2012
    18. Matrimonial Liife  in Islam                                                      2016
    19.                                                                                            2016
    20.                                                                                            2017
    21.                                                                                            2017
    22. Ladaban Zama Da Kishiya A Musuluci                                 2019
    23. Kamanin Annabi Siffofinsa da Ɗabi’unsa Domin Koyi da shi  2020

    B. Maƙaloli:

    1- “Zakatul As’humi Was Sanadat, Wat ta’amulu Biha Fis Shari’atil Islamiyyah”

    Journal of Islamic Studies vo1: 1 NO:1, 2007.

    2- Murabaha to the Purchase Order in the Juristic Perspective

    “Bai’ul Murabahati Li Amirin Bis Shira’i.

    Jornal of Islamic Sturdies

    Department of Islamic Studies, BUK.

    A paper presented at a conference organized y Al Muntada Nigerian Office 1998

    1. Islami Foundation of Nngeria, Kano.
    2. Concil of Ulama, Kano.
    3. Hudabiyya Fondation Kano.
    4. Council for Adult Islamic Education in Rural Areas, Kano State.
    5. Wakili a kwamatin masallacin Jami’ar Bayaro.
    6. Gamayyar Ƙungiyar Haɗakar Bankin Ruwa.
    7. Haɗakan Zuriyyar Malam Isma’ila Yakasai.

    Alhamdu lillah. A yanzu Yahaya Tanko Yana Bayar da darasai na littafai huɗu  a mako, a masallacin Umar bin Khaɗɗab da da littafan Sahihul Bukhari da Fathul Majid a masallatan Nana A’isha da na Khalid binil Walid a unguwar  Dukawuya FCE.

    A yanzu Allah ya azurta Yahaya Tanko da zuryya mai yawa, ‘ya’ya da jikoki.

    Ya yi ritaya a watan Febreru na shekara 2015 daga Jami’ar Bayero ta kano. Amma ya kama aikin kwantiragi da jami’ar Yusuf Maitama sule ta Kano.

  • Tushen Zaman Lafiya Da Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

    Tushen Zaman Lafiya Da Hanyoyin Tabbatar Da Adalci

    Hanyoyin Tabbatar Da Adalci – Majaddid shaihuna Usman ɗan Fodiyo Allah ya ƙara rahama a gare shi; ya rubuta littafi mai suna; “Usulul adli liwalatil umuri wa ahlil fadli” – wato Ginshiƙan kafuwar adalci domin shugabanni da manyan mutane.

    A cikin wannan littafi, ya yi bayanin hanyoyi goma waɗanda in dai shugabanni daga sama har ƙasa za su yi bi su; babu makawa za su kasance masu adalci a shugabancinsu.

    A taƙaice ga waɗannan ginshiƙai na hanyoyin tabbatar da adalci;

    Tushe Na Ɗaya

    Shugaba ya san matsayi da darajar shugabanci da yake yi. Ya sani cewa shugabanci ni’ima ce babba; wacce in ya yi gaskiya da adalci za ta kai shi ga samun ni’ima madawwamiya a lahira da kyakkyawan suna a duniya. Idan kuwa aka samu akasi to zai gamu da matsananciyar azaba a duniya da lahira; saboda haka kada ya yi wasarere da shugabanci ya riƙe shi ƙam ƙam ya yi da gaske ba wasa.

    Tushe Na Biyu

    Lallai ne shugaba ya ja malamai masu tsoron Allah da aiki da iliminsu masu son alhairi ga al’umma masu faɗar gaskiya marasa tsoro marasa kwaɗayi, ya ja su a jikinsa ya rinƙa neman shawarwarinsu da fatawa akan al’amuran shugabancinsa; ya kuma rinƙa amfani da shawarwari da nasihohi da suke yi masa.

    Haka kuma ya nemi masana ƙwararru a kowane fanni na rayuwa kamar manyan ‘yan kasuwa; tsofaffin shugabanni, da ma’aikata na kowane ɓangare dattawan gari har ma da matasa maza da mata masu tsoron Allah da kishin ƙasa domin ya amfana da iliminsu da ƙwarewarsu a fannonin rayuwa da sauransu.

    Tushe Na Uku

    Kasancewarka mai gaskiya da riƙon amana da adalci ba zai kuɓutar da kai ba a wurin Allah; sai ka tabbatar mai ma’aikatanka da jami’an gwamnatinka suna da hali irin naka. Amma idan kana ganin ɓarna ka yi shiru; to haƙiƙa sai ka ba da amsa akan wannan ɓarnar; kuma sai an tuhume ka akan duk ɓarnar da akayi kana sane ka yi shiru ayi maka azaba a kanta ranar ƙiyama.

    Tushe Na Huɗu

    Lallai ne shugaba ya kasance mai yawan haƙuri; afuwa da kau da kai ya guji saurin fushi da yanke hukunci cikin ɓacin rai.

    Tushe Na Biyar

    A duk lokacin da za ka ɗauki wani matakai ko yanke hukunci ko shawara ko sanya hannu akan wani ƙudiri; waɗanda suke ƙarƙashinka ka ɗauki kanka a matsayin ɗaya daga cikin talakawa duk abinda ba za ka so a yi maka ba to kada ka yi wa waninka, duk abinda za ka so ayi maka to ka zartar da shi.

    Tushe Na Shida

    Kada ka wulaƙanta talaka da sauran mutane masu kawo buƙatunsu gare ka da koke – kokensu; saboda babban amfanin shugabanci shine sharewa mabiya hawayensu da sauran buƙatunsu da yin abinda ya kamata akansu.

    Tushe Na Bakwai

    Ka yi rayuwa matsakaiciya tare d tsantseni da wadatar zuci kada ka sabawa kanka da zurfafawa da al’mubazzaranci; a wajen jin daɗi da kece raini wannan zai sa ka mance da wahalhalun da talakawa suke ciki zuciyar ka ta bushe; in suna kuka ka rinƙa jin kamar kukan daɗi suke yi. Kana sheƙa dariya abinka.

    Tushe Na Takwas

    Dukannin abinda zai yiwu cikin sauƙi da lumana, kada ka bi hanyar tsanani ne da tursasawa wajen tabbatar da shi. Ana amfani da tsanani kawai a lokacin da sauƙi ba zai yi amfani ba.

    Tushe Na Tara

    A kowane lokaci ka rinƙa tunanin mutuwarka da kwanciyar ƙabari da tashin alƙiyama da musiba da azabobin da suke cikinta; da kuma ni’ima da rahamar da Allah ya tanada ga masu binsa. Ka rinƙa tunanin shin kai a wane ɓangare za ka kasance idan Allah ya tashi alƙiyama.

    Tushe Na Goma

    Ka sanya tsarin shugabanci na Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance madubinka, ma’aunin shugabancinka ka rinƙa kwaikwayonsa gwargwadon ikonka.

    Bayan waɗannan tuwassa goma waɗanda Shaihu Usman ɗan Fodiyo; ya ambata ya kuma ce imamul Gazzali ne ya faɗe su a cikin wani littafinsa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Halaye Da Siffofin Shugaba Nagari danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Raka’a Biyu Kafin Magariba danna nan

  • Nasihohi Goma Ga Masu Kula Da Dukiyar Al’umma

    Nasihohi Goma Ga Masu Kula Da Dukiyar Al’umma

    Duk shugaba ko ma’aikaci ko wani wakilin jama’a da dukiyar al’umma take gilmawa ko shigowa hannunsa to haƙiƙa yana cikin babban haɗarin da babu abinda zai ƙwace shi sai tsananin yaƙi da zuciya wajen kau da kai da haƙuri da kaucewa cin wa wannan dukiya ta hanyar da ba ta halattaba, tare da yawaita addu’ar Allah Ta’ala ya ba shi ikon sauke nauyin da yake kansa da kula da amanar da aka damƙa masa.

    Amfani da wannan nasihohi goma za su taimaka ƙwarai da gaske wajen tabbatar da haka;

    1) Ka kasance mai imani da cewa dukkanin dukiya ta Allah ce shi kaɗai kai matsayin wakili kawai kake, shi ne ma ya sa aka shata maka dokoki da sharaɗai kan yadda za ka yi mu’amala da wannan dukiyar kuma za a bincike ka a kan hakan ranar lahira. Saboda haka ka tabbatar duk abinda zai zo hannunka ka tabbatar halal ne tsantsa kuma ka yi amfani da shi ta hanyar da ta dace da shari’ar Allah Ta’ala.

    2) Ka kasance mai imani na gaskiya mai amana da kamewa da wadatar zuci sannan ka san hukunce-hukuncen musulunci, da suka shafi harkokin dukiya da kula da ita da kuma yin aiki da su.

    3) Ka sani cewa dukkanin ɗan ƙasa yana da haƙƙi a cikin dukiyar ƙasa kai ma ɗaya ne daga cikinsu, saboda haka, kada ka nuna son kai ko son zuciya da bambanci wajen baiwa mai haƙƙi haƙƙinsa.

    4) Ka sani cewa kare dukiyoyin al’umma daga sata, salwanta da lalacewa wajibi ne a kan kowa, musamman ma’aikata da shugabanni. Saboda tsaron dukiyar al’umma yana daga cikin manufofin shari’ar addinin musulunci.

    5) Ka guji cin amana da ɓarnatar da dukiyar al’umma ka sani ranar ƙiyama za a bincike kan duk abinda ka mallaka ka yi bayanin ta yadda ka same shi da kuma yadda ka yi amfani da shi.

    6) Ka guji yin amfani da dukiyar al’umma a kan buƙatunka na ƙashin kanka wanda ba su shafi aikinka ba. Misali kada ka rinƙa amfani da motar ofis wajen kai mata ko yara unguwa ko makaranta, ko ka ɗauki wani abu ka kai gidanka kana amfani da shi, ko kuma ka rinƙa amfani da injina ko kayan aikin ofis ɗinka ko ma’aikatarka.

    7) Ka yi mu’amala da dukiyar al’umma kamar yadda ake mu’amala da dukiyar maraya. Duk abinda mutum ya ci daga dukiyar marayu ba tare da haƙƙi ba, ya ci wuta balbal. Wajibi ne a rinƙa juya dukiyar marayu tana ƙaruwa, kuma a yi saboda Allah ba don neman a biya ka ba, sai dai in ka kasance mabuƙaci to sai a rinƙa biyanka ladan aikinka. To albashin ma’aikaci da shugabanni shi ne a matsayin ladansu.

    8) Ka sani cewa kare dukiyar al’umma wajibi ne akan kowa da kowa da kowa ba wai sai shugabanni ba kawai, saboda haka ya wajaba kowa ya bayar da gudunmawarsa wajen yaƙar ɓarnatar da dukiyoyin al’umma gwargwadon ikonsa.

    9) Ka guji ƙoƙarin tara kuɗi ta hanyar amfani da ofishinka, kada ka yi sata, kada ka danne haƙƙin kowa, kada ka karɓi na goro, kada ka ci hanci da rashawa.

    10) Ka sani cewa Allah Ta’ala zai yi maka hisabi kan duk abinda ka aikata a ranar da dukiya da ‘ya’ya da ‘yan uwa ba za su yi wa mara gaskiya wani amfani ba. Yi ƙoƙari ka bar wa ‘ya’yanka halal komai ƙanƙantarsa sai Allah ya sanya masa albarka ya inganta bayanka.

    Kada ka tara haram ka mutu ka bar magada, ba za su yi albarka ba, kuma bayanka ba zai yi kyau ba. Ɗan uwa ka kula da wannan nasihohi ka yi aiki da su za su amfane ka a duniya da lahira. Allah ya sa mu dace amin.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Hanyoyin Ɓarnatar Da Dukiyar Al’umma danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Cin Mutuncin Mutane Da Sunan Hamayyar Siyasa. danna nan.

    Don karanta bayani a kan Yadda Sakamakon Zalunci Yake danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Hanyoyin Ɓarnatar Da Dukiyar Al’umma

    Hanyoyin Ɓarnatar Da Dukiyar Al’umma

    Akwai hanyoyi da yawa da shugabanni da ma’aikata suke bi wajen ɓarnatar da dukiyoyin al’umma kuma sai Allah ya hukunta su a kansu domin nau’i ne na cin amana da rusa tattalin arziƙin ƙasa.

    Kaɗan daga cikin waɗannan hanyoyi su ne;

    1) Fantamawa da wadaƙar da shugabanni da manyan ma’aikata suke yi; da su da iyalansu da abokansu da surukansu da barorinsu da dukiyar al’umma musamman a lokacin bukukuwansu.

    2) Antaya dukiya ga wanda aka ga dama haka kawai; saboda an ga dama ya zama miloniya ya yi nashe-nashe yana muwalat ya zama kamar wani sabon mutum. A can gefe kuma ga talakawa suna ta kuka wasu ma suna mutuwa; an hana su ɗan abinda za su sayi abinci da magani.

    3) Tara dukiyar ƙasa da taskance ta da hana talakawa da sauran mabuƙata sai dai a yi ta cewa tattalin arziƙin ƙasa ya haɓaka; asusun gwamnati ya cika maƙil da kuɗi; amma babu wani talaka da zai gani a ƙwaryar tuwonsa sai dai a yi ta surutu maras kan gado. Wanda in ba su masu faɗar ba, babu mai fahimtar abinda suke faɗa.

    4) Yin amfani da dukiyar al’umma a kan buƙatun ƙashin kai, kamar motoci, injina; kayan aiki da kuɗin al’umma a gonakinsu, ko ma’aikatunsu ko gidajensu da sauransu.

    5) Fifita manya da masu hannu da shuni a kan waɗanda ba su da komai ko ba su san kowa ba; ta hanyar rage, ko yafe musu haraji ko kuɗin fito ko ɗaukar su ko ‘ya’yansu ko matansu aiki; ko ba su bashi don su juya wataƙila ma a ce an yafe musu.

    6) Kashewa mawaƙa da makaɗa kuɗaɗe masu yawa don kawai neman suna; alhali ga malaman makaranta da likitoci da sauran talakawa suna fama da ƙarancin albashi wanda ya jawo taɓarɓarewar aikin gwamnati da rashin zaman lafiya a ƙasa, sai ka ga a lokaci guda wani mawaƙi ko ɗan bal ko wata ‘yar fim suna zama miloniyoyi a sama.

    7) Kashe kuɗaɗe masu nauyin gaske a kan harkokin zaɓe; waɗanda da za a tsakuro ɗaya bisa ukunsu a sa a ɓangaren ilimi ko noma ko lafiya ko tsaro da an ga canji a rayuwar al’umma.

    Amma ina sai a yi watsi-watsi da waɗannan kuɗaɗe masu ciwon gaske a yi abinda aka ga dama; a ce an zaɓe wane ya ci wane ya faɗi.

    8) Kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tarbar shugabanni na gida da na wajen domin ƙawata tituna; tara musu talakawa, shirya abinci da sauran abubuwa na ganin ido sai ka ga a yini ɗaya an kashe miliyoyin nairori na fitar hankali; saboda wai shugaba wane zai kawo ziyara ƙasa ko jiha.

    9) Warewa harkokin wasannin kuɗaɗe masu ɗimbin yawa fiye da kuɗin da aka warewa ma’aikatar lafiya; tsaro, ilimi da sauransu waɗanda suka fi wasanni muhimmanci; amma dai haka suke rufe idanunsu su toshe kunnuwansu su narka kuɗi a can ba ruwan su.

    10) Caɓawa masallatai ado wani lakacin da gwalagwalai amma a yi burus da limamai da ladanai da ma su kansu masallatan masu sallah a wasu masallatan; sai ka ga adon yana shagalar da masu sallah maimakon su tara hankalinsu ga sallarsu; sai su yi ta kallon ƙyale – ƙyalen da aka yi.

    A wasu ƙasashen kuma sai a gina masallaci gari guda amma kuma babu masu sallar, sai dai ‘yan yawon buɗe idanu ne za su rinƙa zuwa suna ɗaukar hotuna a cikinsa.
    Kamar yadda a waɗansu ƙasashen ake ƙawata ƙaburburan shaihunai a kashe miliyoyin daloli domin kawai a samu goyon bayan mabiyan wannan mamacin (shehin).

    11) Rashin kula da aiki ta hanyar zuwa a makare da tashi kafin lokacin ya yi; da ma ƙin yin aikin ai an je wurin aikin sai a ɓuge da hira ko karance-karancen jaridu ko matse-matsen waya da kallon talabijin; ka ga kuɗin da ake kashewa kan waɗannan ayyukan da ma’aikatan kusan duk asarar su ake yi.

    12) Kashe dukiyar al’umma kan bukukuwa na ƙasa ko na siyasa ko bukukuwan da ake danganta su ga addini kamar bikin ranar samun ‘yancin kai, Bikin ranar demokuraɗiyya; bukukuwan mauludin Annabi da na shaihunai, sai ka ga an fitar da miliyoyin kuɗi an yi watandar su, alhali ga lalurorin rayuwa babu cikakkiyar kulawa.

    13) Biyawa ‘yan siyasa da ‘yan jagaliya aikin hajji ba don komai ba sai don kawai sun yi wa shugaba yaƙin neman zaɓe sai ya saka musu da kujerun hajji, waɗansu ma in sun je hajijiya kawai za su yi su dawo. Amma malamai masu koyar da alhazai aikin hajji da likitoci da sauran maa’aikatan da za su taimakawa alhazai su yi ibada cikin nutsuwa da inganci waɗannan babu wani laifi don gwamnati ta biya musu aikin hajji amma a ji tsoron Allah a yi gaskiya da adalci a dubi cancanta wajen zaɓar waɗanda za a biyawa.

    14) Ha’inci wajen ba da kwangila ta hanyar kashe-mu-raba tsakanin ‘yan kwangila da jami’an gwamnati; sai a zaftare kuɗin ko dai a ƙi yin aikin sam ko kuma a yi shi mara inganci ta yadda da an kwana biyu zai tashi daga aiki, in titi ne sai ya ɓaɓɓagure in gini ne ya rushe in wasu injina ne su lalace. Subhanallah.

    15) Wawashe kuɗaɗen al’umma a je a damfare su a bankunan ƙasashen turai, su yi ta gina kansu da su; ‘yan ƙasa kuma suna ta mutuwa. Waɗansu ma sai su je can su kafa masana’antu alhali ga miliyoyin ‘yan ƙasa ba su da aikin yi.

    16) Tarukan siyasa musamman na neman zaɓe da karɓar waɗanda suka baro jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar gwamnati; in ka ji yawan kuɗin da ake kashewa a irin wannan harkar abin akwai matuƙar takaici da ɗaure kai.

    17) Ware kuɗi mai yawan gaske da sunan wai za a yi addu’ar neman zaman lafiya ga ƙasa; ko kuma samun nasara a zaɓe. Sai dai abin takaicin shi ne mafi yawancin wannan kuɗi masu addu’ar ta gaske; saboda Allah ko labarinsu ba su ji ballantana su gan su. Sai a a yi dumbuza ana bai wa bokaye da miyagun malamai da matsafa da waɗanda ma ba musulmi ba. In ya zama dole sai an fitar da wannan kuɗi kamata ya yi a bi talakawa da gajiyayyu da malaman zaure da na tsangayu da ɗalibansu a ba su abinda zai faranta musu rayuka su ma su sami sa’ida da walwala to ko ba su yi addu’a ba; Allah zai biya buƙata sakamakon faranta musu da aka yi.

    A gaskiya hanyoyi da waɗansu shuwagabanni suke bai wajen tarwatsa da ɓarna da dukiyar al’umma suna da yawan gaske, abin fa ya zama sai dai a ce innalillahi wa inna ilaihirraji’un.
    Ya Allah ka ba mu ikon gyaran halayen mu, ka yi mana a fuwa da gafara ka a zurtamu da shugabanni managarta masu ƙarfi da amana amin.

    Domin karanta cikakken bayani akan Hidisai Goma Kan Hatsarin Shugabanci danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Haramcin Zalunci, Tasirin Addu’ar Wanda Aka Zalunta Da Wajabcin Sa danna nan.

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Addu’a Ga Yaran Da Ba Sa Ji

    Addu’a Ga Yaran Da Ba Sa Ji

    Yaron da ake gani ya ɗauko hanyar lalacewa ba ya jin magana; ba a sa shi ya yi kuma ba a sa shi ya bari, to ga wata tajriba da ya kamata uwa ta yi wa yaranta.

    Ranar Juma’a rana ce mai tsada. Shi ne lokacin sallar la’asar, duk addu’ar da kika yi a lokacin tana da tasiri ga wanda aka yi wa. A wata ruyuwar ma an ce Annabi Yaƙuba (Alaihis Salam) ya yi wa ‘ya’yansa addu’ar neman gafarar kuskuren da suka aikatawa ɗan uwansu Yusuf bayan Allah ya bayyanar da shi, don haka lokaci ne mai daraja.

    Ana son bayan kin yi sallar la’asar ki sami ruwan zamzam ko kuma na rijiya ko kuma wanda kika yi alwala kika rage.

    Bayan kin idar da sallarki cikin addu’arki sai ki karanta wannan addu’ar kamar haka;

    “Ya maliku yaumud din, iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in, ihdina siraɗal mustaƙim, siraɗal ladhina an amta alaihim, gairil magdubi alaihim waladdaaliin”

    Sai ki roƙi Allah ya tsare miki yaranki ko yarinyarki tare da kiran sunanta ko sunanshi. Ki yi shi adadi mai yawa kya iya yin ɗari 100, kina karantawa kina tofawa cikin ruwan. In kin gama sai ki ƙara tahiya ita ma ƙafa ɗari 100 ki tofa cikin ruwan. Akan so kullum ki yi wannan har sai wata Juma’ar ta zagayo, kina yi kina tara ruwa. In kin gama sai ki rinƙa ba shi ruwan yana sha da safe kafin ya ci abinci haka da daddare kafin ya kwanta bacci. Inkuma ya yi kangarewar da ba zai sha ba, sai ki sarrafa masa a cikin abinci ya ci ya sha. Za ki ga mamaki yadda yaronki zai koma In Sha Allah.

    Domin karanta cikakken bayani akan Matakan Da Za A Bi Domin Hana Yara Shaye-shaye danna nan.

    Don karanta Hukunce-hukuncen Ƙananan Yara danna nan 

     

     

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Matakan Da Za A Bi Domin Hana Yara Shaye-shaye

    Matakan Da Za A Bi Domin Hana Yara Shaye-shaye

    Akan kai wani mataki duk irin kulawar uwa ko kuma kulawar uba ya zamto yaransu ko yarinyarta ta fanɗare.

    Ka ga yaro ya jefa kansa cikin wannan hatsarin rayuwa, yaro ya rinƙa shaye-shaye sakamakon abokai da ya gamu da su.

    Ga matakan da ake bi In Sha Allah zai daina:

    1. Matakin farko raba shi da abokan hurɗarsa a sama masa wajen sana’a.

    2. Mataki na biyu shi ne ana ɗaukan ayoyin sakina na Al ƙur’ani gaba ɗaya da kuma ayatus Sam, a karanta su a tofa a ruwan sama ko na rijiya, sannan a samu za’afaran da ganyen magarya da muski ɗan kaɗan sai a ba shi ya rinƙa sha da safe da kuma dare.

    Sannan za a iya ɗaukan dukkan nau’in kayan mayen da yake sha a haɗa su guri guda; anemo garin kustul hindi cokali uku da kuma man zaitun da man habba da kuma man kwakwa da na tafarnuwa da na’a na’a a haɗa su guri guda da kayan shaye shaye sannan a rufe a bar su su kwana.

    In gari ya waye a girgizasu sosai, sai a tace sannan a ba shi kafin ya ci abinci. Ana so da ya sha ya yi amai. Wannan haɗin ana so a rinƙa ba shi duk bayan sati uku ko kuma wata ɗaya. Sannan a haɗa da wannan ruwan da aka yi tofin ayoyin a ciki. Insha Allah duk abinda yake sha zai fita daga ransa ya dawo cikakken mutum.

    Minhaj 274
    Ayatus Sakina: Minhaj 255

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Haddar Karatu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Karatun Manzon Allah danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Falalar Yaɗa Sallama A Cikin Al’umma

    Falalar Yaɗa Sallama A Cikin Al’umma

    Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; ‘Ba za ku shiga aljanna ba sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba sai kun so juna. Shin ba na nuna muku wani abu da in kun yi shi za ku so juna ba? Ku yaɗa sallama tsakaninku’.

    Ammar, Allah ya yarda da shi, ya ce: Abubuwa uku, wanda duk ya haɗa su, ya haɗa imani; mutum ya yi adalci ga kansa, da yaɗa gaisuwar sallama a cikin al’umma, da yin kyauta a cikin rashin wadata’.

    Daga Abdullah ibn Umar, Allah ya yarda da shi, ya ce: wani mutum ya tambayi Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam); wane abu ne a cikin musulunci ya fi alheri? Sai ya ce; Ka ciyar da abinci, kuma ka yi sallama ga wanda ka sani da wanda ba ka sani ba’.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Amsa Wa Kafiri Idan Ya yi Sallama danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nafilolin Sallah. danna nan.

    Don karanta cikakken bayani a kan A Ina Mahaifiyar Annabi muhammad (S.A.W) Ta Rasu? danna nan.

  • Addu’o’in Neman Tsayar Da Ruwan Sama

    Addu’o’in Neman Tsayar Da Ruwan Sama

    “Allaahumma hawaalainaa walaa alainaa, Allaahumma alal akaami wazziraabi, wa buɗuunil waudiyati, wa manaabitis shajari”.{Ya Allah! Ka sanya shi ya zuba a kewayenmu, ba a kanmu ba. Ya Allah! Ka sanya shi a kan jigayi da duwatsu, da cikin rafuka, da wajen saiwoyin itatuwa}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Ganin Jinjirin Wata danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunnah wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Abubuwan Da Sai Da Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe

    Abubuwan Da Sai Da Su Aure Yake Zama Karɓaɓɓe

    (1) Samuwar Amincewar Waɗanda Za A Ɗaurawa Aure

    A shari’ance, aure ba ya zama zartacce, abin la’akari da shi, sai idan an sami yardar ma’aurata da kuma amincewarsu. Dalili kuwa faɗar Allah Maɗaukaki: “Ku auri abin da ya kwanta muku a rai daga matan (da suka halatta a gare ku), biyu-biyu ko uku-uku ko kuma hudu-hudu.

    Da kuma hadisin da aka karɓo daga Ukbatu ɗan Amir (Allah ya yarda da shi) ya ce “Haƙiƙa Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce: “Da wani mutum (da zai ɗaurawa aure ), ka yarda in aura maka wance? Sai ya ce: “Eh (na yarda)”, sannan Annabi ya ce da matar: “Kin yarda in aura miki wane? Sai ta ce, “Eh (na yarda)”, Sai Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ɗaura musu aure”. ( Baihaƙi da Hakim da wasunsu ne suka rawaito shi ).

    Kuma Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya yarda da shi) ya ce: “Haƙiƙa, wata budurwa ta zo wajen Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ta ce: mahaifinta ya ɗaura mata aure (Da wani), ba da son ranta ba (nan take) sai Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi), ya ba ta zaɓin idan ta amince da wanda aka aura mata auren ya ɗauru, idan kuma ba ta son sa, to auren bai ɗauru ba”. ( Ahmad da Abu Dawud da wasunsu ne suka rawaito shi).

    Sannan an karɓo daga Khansa’u ‘yar Khidan (Allah ya yarda da ita) Cewa: mahaifinta ya ɗaura mata aure da wani tana bazawara, ba da son ranta ba, sai ta je ta shaida wa Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) sai ya ce, “Auren bai ɗauru ba”. ( Bukhari ne ya rawaito shi ).

    (2) Waliyyin Matar Da Za A Aura

    Waliyyi shi ne mutumin da alhakin aurar da mace yake wuyansu, kamar uba, ko madadinsa, ko shugaban musulmai. Waliyyi ma sharaɗi ne daga sharuɗan da sai da su aure yake ɗauruwa a Musulunce. Saboda haka, bai halatta mace ta aurar da mace ba, kamar yadda bai halatta mace ta yi gaban kanta ta aurar da kanta ga wani ba.

    An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya yarda da shi) ya ce: “Manzon Allah ( tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce : “Mace ba ta aurar da mace, haka kuma mace ba ta aurar da kanta”. ( Ibn Majah ne ya rawaito shi ). Kuma an karɓo daga Ikrima da Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya yarda da su) sun ce: “Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: ” Babu aure sai da waliyyi”.

    Sannan kuma an karɓo daga A’isha (Allah ya yarda da ita) ta ce: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Duk matar da ta yi aure ba da izinin waliyyinta ba, auren ɓatacce ne. Idan kuma wanda ya aure ta a kan hakan, har ya sadu da ita, to, ya ba ta sadakinta, saboda saduwar da ya yi da ita. Idan kuwa mace da waliyyinta suka saɓa, to, shugaban musulmai shi ne waliyyin duk wacce ba ta da waliyyi”. (Abu Dawuda da Ibn Majah ne suka rawaito shi).

    (3) Shaidu

    Su kuwa shaidu su ne adalan mutanen da suke halartar gurin ɗaurin aure, su kuma kasance a gurin a lokacin da za a ɗaura auren. A Musulunce, mutane biyu su ne mafi ƙarancin shaidu game da ɗaurin aure. Saboda hadisin da aka karɓo daga Imran ɗan Husaini, da A’isha (Allah ya yarda da ita) cewa, Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Babu aure sai da waliyyi da kuma shaidu biyu adalai”. (Imam Ahmad ne ya rawaito shi).

    Amfanin Samar Da Shaidu A Aure:

    Yana daga cikin amfanin da samar da shaidu yake da shi:
    1. Kawar da zargin zina, ko daduro tsakanin ma’aurata.
    2. Hana a kira ‘ya’yan da mutum ya Haifa ‘ya’yan zina (shegu).

    (4) Sadaki

    Sadaki shi ne dukiyar aure, wacce mace take cancantarsa daga wajen miji ta dalilin aure. Saboda faɗar Allah Maɗaukaki: “Ku ba wa mata sadakinsu cikin daɗin rai, idan kuma suka sayar muku da wani abu daga cikinsa da sonsu (don kansu), to, ku ci shi (halak malak ) rai kwance”. Da kuma faɗar Allah maɗaukaki: “To, waɗanda kuka ji daɗi da su daga cikinsu (mata) ku ba su sadakinsu (cikakke) tilas”.

    Sannan kuma Allah da hikimarsa da ya yi bayinsa, bai yi su bai ɗaya ba, don haka ma, da ya wajabta musu bayar da sadaki, sai bai iyakance musu shi ba. Saboda ya dace da mai hali da kuma mai ƙaramin ƙarfi. Kowanne gwargwadon halinsa. Don haka, a Musulunce ya halatta mutumin da yake da hali ya dunƙule wasu maƙudan kuɗi ya bayar a matsayin sadakin matar da zai aura.

    Allah Madaukaki ya ce : “Idan kuka yi nufin musanya wata mace a maimakon wata (da kuka saka) alhali kuwa da kun ba wa ɗayarsu (ta farkon) dukiya mai ɗimbin yawa (a matsayin sadakinta), to, kada ku karɓi komai daga cikinsa, shin kwa karɓe shi don zalunci da saɓo mabayyani”.

    Sai dai kuma mafi falalar sadaki shi ne wanda bayaninsa ya zo kamar haka:
    An karɓo daga Ukbatu ɗan Amir (Allah ya yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) “Ya aura wa wani mutum mace a kan sadakin zobe na ƙarfe”. (Hakim ne yarawaito shi). Bayan haka kuma, shi sadaki haƙƙi ne na matar da aka aura, kamar dai yadda bayani ya gabata. Saboda haka, bai halatta ba ga waninta ya ci wani abu daga cikinsa, sai dai inda izininta.

    To bayan kammalar bayanin waɗannan abubuwa da muka ji, ana so a lokacin da za a gudanar da ɗaurin aure a kwaikwayi Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) a rigayi ɗaurin auren da gabatar da wannan addu’ar kamar haka: An karbo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Allah ya yarda da shi) ya ce: Manzon Allah (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya koya mana yin “Huɗubar Haja” a lokacin ɗaurin aure. Wato:

    “Innal hamdulillahi ta’ala, nahmadhu wanastagiynuhu, wanastagfiruhu, wa na’u’zu billahi min shuruwri anfusina wa min sayyi’a’ti a’a’malina, man yahdihil-llahu fala mudilla-lahu, waman yudlil fala hadiyaya lahu, wa’ashadu an lailahaillallahu wahdahu la shariyka lahu, wa’ashadu anna muhammadan abduhuwarasuluhu.
    Ya ayyuhal lazina a’manuttaƙuwllaha haƙƙa tuƙatuhi wala tamutunna illa wa antum muslimun (Al-i-mran, aya ta (102)

    Ya ayyuhannasu-ttaƙuw rabbakumullazhiy kalaƙakum min nafsin wahida wakalaƙa minha zaujaha wabassa minhuma rajalan kasiran wa nisa’a’wattaƙuwllahal lazhiy tasa’a’luna bihi wal’arhama innallaha kana alaikum raƙiyba (An nisa’i aya (1)

    Ya ayyuhal-lazhina ‘a’manuttaƙuw-llaha wa ƙulu ƙaulan sadhidhan yuslih lakum a’a’malakum wa yagfir lakum zhunubakum waman yuɗi’illaha wa rasuluhu faƙad faza fauzan a’zhima (Al Ahzab) Abu Dawud, da Nisa’i da wasunsu ne suka rawaito shi.
    Sannan kuma ya halatta, bayan gama ɗaura aure, ranar a kai amarya gidan miji, a buga dundufa domin sanar da aure da kuma faranta ran ango. Amma bai halatta a yi rawa ba.

    Ranar Haɗuwar Ango Da Amarya:

    A Musulunce ana so ranar da ango ya fara haɗuwa da amaryasa ko kuma ranar da aka kawo wa ango matarsa gidansa, ya yi ƙoƙarin yin waɗannan abubuwa masu zuwa kamar haka:

    (1) Ango ya jagoranci matarsa su yi Sallah raka’a biyu- nafila don miƙa godiyarsu ga Allah da ya cika musu burinsu kamar yadda Ibn Abi Shaiba ya rawaito.

    (2) Ya ɗora hannunsa a kan goshin matarsa, wato ya karanta ya riƙe, sannan kuma ya karanta wannan addu’a kamar haka:
    “Ya Allah ina roƙonka alherin wannan mata da alherin da ka halicceta a kansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin abin da ka halicceta a kansa”. ( Bukhari a cikin littafinsa da Abu Dawuda da Ibn Majah da wasunsu ne suka rawaito shi ).

    (3) Gabatarwa da amarya wani ɗan abin kusa da baka, kamar yadda Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya yi wa matarsa A’isha (Allah ya yarda da ita ).

    (4) Goge baki kafin kwantawa da amarya, domin kawar da wani hamami, ko wari da ka iya tashi daga cikin baki. Kamar yadda aka samu Muslim da Abu Awana sun rawaito Annabi (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya yi haka.

    (5) Yin addu’ar saduwa da mace, kafin fara saduwa da ita. Addu’ar kuwa ita ce: ” Ya Allah ka nesanta ni daga shaiɗan ka kuma nesanta shaiɗan daga abin da ka azurta ni da shi”.
    Annabi ( Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) ya ce: Idan Allah ya hukunta wa miji da matarsa samun ɗa a saduwar da suka karanta wannan addu’ar, to, shaiɗan ba zai cutar da ɗan da suka samu ba har abada”. (Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ).

    (6) Yin walima da abin da Allah ya hore, bayan tarewa da saduwa da amarya. Saboda aiwatarwar Annabi da kuma umarnin da ya yi na a yi walima.

    Sannan kuma idan za a kira jama’a walima, to a yi ƙoƙarin ganin an tara waɗanda suke mabuƙata, saboda Annabi (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ) yana cewa: ” Mafi sharrin abincin walima, wanda ake kiran (ko gayyatar) mawadata a ƙyale mabuƙata “. (wato a ƙi gayyatarsu). ( Malik da Bukhari da Muslim da wasunsu ne suka rawaito shi ).

    Daga lokacin da Allah ya hukunta wa musulmi aurar wata mace, ko kuma ya hukunta wa musulma auren wani musulmi, to ya zamar musu lallai su san cewa, a Musulunce akwai wasu nauye-nauye da suke tattare da rayuwar da za su fuskanta ta zaman aure, waɗanda suka sha bamban da na irin rayuwar da suka faro a baya ta zaman kaɗaici.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nauye- Nauyen Rayuwar Aure danna koren rubutun nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Nagartacciyar Rayuwar Aure wanda Abubakar Abbas ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna koren rubutun nan.

    Edita@rumasau-kallamu