Tatsuniyar ‘Yan Bakwai Da Aljana

0
39

Ga ta nan, ga ta nanku.

A can kusa da dajin aljannu wanda aka ce ya yi iyaka da bangon duniya, akwai wata mata mai ’ya’ya maza su bakwai. Ana nan, ana nan sai yaran suka girma, har dai suka isa aure. Da gyatumarsu ta ga sun isa aure, sai ta tara su ta ce: “Ya kamata a ce yanzu kun yi aure, tunda ga shi Allah ya sa duk kun girma, kowa ya mallaki hankalinsa.”

Da suka ji haka, sai babban cikinsu ya ce wa uwar: “Za mu yi aure, amma muna so a sama mana ’yan mata bakwai waɗanda suke uwarsu ɗaya.” Sai babarsu ta ce: “Kash, amma ai duk garin nan babu irin ’yanmatan da kuke so, sai dai ku tlafi nema wani garin.”

Sai suka bi maganar mahaifiyarsu, suka shirya suka kama hanya za su neman matan aure. Bayan ’yan bakwai sun bar gari sun kama hanya, sun yi tafiya mai nisa, sai suka haɗu da wata mata da ’yarta ɗaya suna noma. Da ta ga samari bakwai rigis, sai ta ɗaga kai ta dube su tace: “Sannunku samari.” Su kuwa suka amsa gaisuwarta a cikin ladabi.

Sai ta tambaye su inda za su. Sai babbansu ya ce mata: “Za mu je neman matan aure ne.” Da ta ji haka sai ta ce: “To ga ’yata idan za ku aura.” Tare da ban girma sai ɗaya daga cikinsu ya ce: “A a, muna neman ’yan mata bakwai ne waɗanda suke uwarsu ɗaya kamar mu.” Wannan bayani ya rufe mata baki, sai ta ce: “To, shi ke nan; ni dai
’yata ɗaya ce idan za ku karɓe ta.”

Sai suka ce: “A a, mun gode.” To ashe wannan mata aljana ce ba su sani ba. Da suka yi nisa daga inda take, sai ta yi irin saurin aljannu ta je can gabansu a wata gonar da ’ya’ya mata biyu. Saboda suna da ladabi da girmama manya, a nan ma suka gaishe ta, ba tare da sun san ita ce ba, saboda ta sauya kama. Matar nan ta tambaye su labarinsu, suka faɗa mata tare da bayani a kan abin da suka fito nema.

Sai ta nuna za ta ba su ’yanmatan nan biyu idan sun amince. A nan ma dai a cikin hikima suka yi mata bayanin cewa ’yan mata bakwai ’yan ciki ɗaya suke nema. Suka wuce suka bar ta a wannan gonar. Da matar nan ta ga sun wuce, sai ta ɓata, ta je gaba ta ƙara sake kamanni. Ta shiga wata gonar tare da ’yan mata uku.

Haka dai ta dinga yi musu har sai da suka kai biyar. Sai suka ce su fasai sun sami ’yan matan da su ma bakwai ne kamar su. Sai aljana ta sake ɓata, ta rikiɗa ta zama wata mata kyakkyawa mai ’ya’ya mata bakwai suna taya ta noma. Da samari bakwai suka zo za su wuce sai matar ta yi musu sallama. Da suka gaisa sai ta tambaye su inda za su.

Kamar yadda suka saba yin bayani a baya, sai suka ce za su neman aure ne, to amma sai ’yan matan da zasu aura ɗin sun kai bakwai, kuma ’yan ciki ɗaya kamar su. Da jin haka sai ta ce wa babban cikinsu: “To tun da mun haɗu ni ma ina da ’yan mata bakwai ’yan ciki ɗaya kamar ku, in kun yarda sai in haɗa ku.” Sai baki ɗaya suka amsa mata: “Yawwa; yanzu muka sami matan da za mu aura.”

Daga nan sai matar nan ta kai su gidanta, ta sa ’yan matan suka yi wa samarin nan ruwa. Da suka ɗebo ruwa suka kawo, sai kowacce ta ba wanda za ta aura; amma fa ruwan ba ruwa ne na gaske ba, duk jini ne, in ban da na ɗan’auta; shi yarinyarsa ba ta kawo masa ruwan jini ba.

Da ’yan matan suka tafi sai ɗan’autansu ya ce kada su sha ruwan da aka ba su saboda jini ne, ba ruwa ba. Da sauran suka ji haka, sai suka zubar, ya ba su nasa suka sha suka ƙoshi. Can kuma sai ’yan matan suka shiga dafa wa baƙinsu abinci. ’Yan mata shiɗa suka ɗebo naman mutane da uwar ta yi tanadi, suka shiga dafa wa samarinsu; amma ƙaramar cikinsu ta ɗan’auta, sai ta ɗebo naman shanu ta girka wa masoyinta ɗan’auta.

Da suka dafa abinci suka kawo wa mazajensu, sai da aka zo cin abinci, ɗan’autansu ya ce su zubar da abincin domin da naman mutane a ciki. Da suka zubar sai ya kawo musu nasa suka ci, har suka ƙoshi. Da dare ya yi, sai aka nuna wa kowannensu ɗakinsa shi kaɗai. Amma ɗan’auta da amaryarsa sai suka shiga wata bukka.

Can bayan duk sauran sun yi barci, sai surukarsu, watau aljana ta fara wasa wuƙarta domin ta riga ta yanke shawara idan dare ya yi za ta yanka su duka. Saboda ɗan’auta ya san abin da matar take son yi, sai ya zagaya ya shiga kowane ɗaki, yana cire wa mazan kayansu yana sa musu na mata, su kuma matan yana sanya musu kayan mazan.

Da ya gama, ya koma ɗakinsa ya shirya ya kama tona rami har zuwa garinsu. Da ya gama sai ya kwanta yana sauraron matar nan ta dinga shiga ɗaki-ɗaki tana yanka ’ya’yanta ba tare da ta sani ba. Da ɗan’auta ya tabbatar matar ta gama yanke-yanken ta koma, sai ya fita ya tashi duk ’yan’uwansa don su gudu.

Sai suka shiga ramin da ya tona suka tafi gida. Ita kuwa aljana da gari ya waye sai ta fara buga ƙofofin ’ya’yanta don su tashi, amma shiru. Da ta karairaya ƙofofin ta shiga ɗakunan, sai ta tarar ashe ’ya’yanta ne ta yanka gaba ɗaya. A nan take ta fara kuka. Da ta ɗan huce, sai ta ce sai ta yi maganin yaran nan.

Sai ta rikiɗa ta zama goɗiya ta shiga garin ’yan bakwai. Da ta je daidai gidansu sai suka gan ta. Sai ɗan’auta ya ce a bar shi ya kama ta, sai babbansu ya ce: “Ai kai ne ƙarami don haka bai kamata ka kama goɗiyar nan ba.” Sai ya bari babbansu ya kama ta ya ɗaure ta cikin gidansu yana kiwonta, har ta yi ƙiba, ta yi kyau.

Bayan wasu kwanaki sai ɗan’auta ya ce da yayansa: “Yau zan kai maka goɗiyarka rafi.” Sai ya ce: “To, na gode.” Sai ya kwance goɗiya ya kai rafi ya ɗaure a jikin bishiya; sai ya samo wata babbar sanda ya fara jibgar goɗiyar nan yana waƙa yana cewa: “Ba goɗiya ba ce, aljana ce.”

Ya doke ta sosai har ta rame. Da ya koma gida da goɗiyar sai yayansa ya ga duk jikinta jina-jina, kuma ta rame. Ganin haka sai yayan nasa ya kama shi da faɗa. Sai ɗan’auta ya ce: “To shi ke nan, muna nan da kai za ka zo ka yi da-na-sani.” Washe-gari sai babban wan su ɗan’auta ya hau goɗiyar domin ya kai ta rafi shan ruwa.

Amma da goɗiyar ta ga sun fita daga cikin gari, sai ta kama sukuwa kamar za ta tashi, ba ta tsaya ba sai a gidan aljanar da ta so yanka su. Tana isa ta zame, ya faɗo ƙasa, kuma ta rikiɗa ta koma siffarta ta aljana. Sai ta dube shi tace: “’Yan banza; ni kuka kashe wa ’ya’ya, to duk sai na cinye ku. Tashi ka jiƙa waccan tokar miyar don zan dafa ka da ita in an jima da daddare.”

Sai ya tashi ya jiƙa tokar miya; sai aljana ta ce: “Zauna kusa da tokar don da ita zan dafa ka.” A can gida ba a ga yayan ɗan’auta ya dawo ba, sai ɗan’auta ya rikiɗa ya koma ɗan maraƙi ya je gidan aljana. Daga shiga sai ya nufi inda ɗan’uwansa yake zaune, ya ture tokar da ke gabansa.

Da babban ya ga haka sai ya ce wa aljana: “Kin ga ɗan maraƙi ya zo ya zubar da ruwan tokar.” Sai aljana ta ce: “Maza ka kwashe ka kai can waje, ka dawo ka sake jiƙa wata.” Shi kuwa sai ya bi umarninta. Ya kori ɗan maraƙi waje, sai ya sake jiƙa toka ya zauna a gefe. Yana zaune sai ɗan maraƙi ya sake zuwaya zubar da ruwan tokar.

Sai ya tashi ya kirawo aljana ya gaya mata cewa ɗan maraƙin nan ya sake zubar da ruwan tokar. Sai aljana ta ce: “To ka kora shi ka kai shi bakin gangaren can mai
nisa.” Da ya kora ɗan maraƙi har suka yi nisa da gidan aljana, sai ga ɗan maraƙi ya koma ɗan’auta. Sai ya dubi yayansa ya ce: “Ai dama na gaya maka ka yi hankali da goɗiyar nan.”

Ba dai tare da ɓata lokaci ba sai ya ce da yayansa su tafi gida. Nan da nan suka kama hanya. Can da aljana ta ga shiru, sai ta bi sawu, sai ta ga alama lallai sun gudu. Sai ta ce: “Zan yi maganin ɗan’auta.”A nan take aljana ta rikiɗa, ta zama kyakkyawar budurwa ta shiga garin su ’yan bakwai, tana tafiya har ta kai ƙofar gidansu. Da suka gan ta sai suka ce dukkansu kowa yana son ta, amma daga ƙarshe suka amince a bar wa yayansu ita.

Suka bar masa, aka ɗaura musu aure. Da dare ya yi suna ɗaki da matarsa sai ya ga ta rikiɗa ta zama aljana; sai ta ce: “Kun ɗauka za ku tsira daga sharri na ne?” Kafin ya ma gane abin da yake ciki, sai ta yi farat ta ƙwaƙwale masa ido, ta tafi da shi. Da gari ya waye aka buga ƙofa, sai aka ji shiru. Ɗan’auta ne ya kira yayansu ya amsa, sai ya gayawa ƙannensa amarya ta ƙwaƙwale masa idanu.

Ɗan’auta ya ce shi kenan, ya san abin da zai yi; ya kama hanya ya je bakin rafi ya cika cikinsa da ruwa, ya rikiɗa ya zama tsohuwa, ya yafa mayafi ya tafi gidan aljana. Da ya isa ya yi sallama, sai ta amsa. ’Yar tsohuwa ta shiga ta ce wa aljana ta ji an yi mata rasuwa shi ya sa ta zo yi mata gaisuwa, kuma ta ƙara ba ta haƙuri da rashin da ta yi.

Da aljana ta ji jawabin tsohuwa, sai ta yi mata godiya, kuma tace: “To me zan ba ki ne tsaraba tun da kin zo yi mini ta’aziyya daga nesa?” Sai tsohuwa ta ce: “Haba babu komai, sai dai ina da wata matsala da ta dame ni.” Da aljana ta ji haka sai ta ce: “Wace irin matsala ce?” Sai tsohuwa ta shiga marairaita ta ce wai yau mijinta ya yi shekara da shekaru ba shi da ido, da yana gani ma da tare za su zo gaishe ta.

Da ta ji wannan sai ta ce wa tsohuwa: “Haba ai babu komai; ina da wasu idanu da na ƙwaƙwalo na zo da su jiya. Sai ki ɗauka, idan kin je gida ki jiƙa su a rama ki sa masa su.”
’Yar tsohuwa ta yi godiya, ta ɗebi idanu ta kama hanya. Da ta fita waje sai ta rikiɗa, Ɗan’auta ya koma kamanninsa na farko ya ƙyalkyace da dariya.

Ashe aljana ta gane shi ne ya zo; sai ta ji haushi ta ce: “Na san yadda zan yi da shi da ’yan’uwansa.” Da ɗan’auta ya je gida, sai ya samo rama ya jiƙa idanun, ya sanyawa yayansa, nan da nan ya fara gani. Ana nan sai wata rana ’yan bakwai suka tafi daji su yanko ciyawa. Da suka yanka, sai kowa ya ɗaure tasa, amma sai ɗan’auta ya ga wani babban maciji ya shiga ta yayansu.

Sai kawai yace: “Yaya ka bar mini taka zan ɗauka, kai ka ɗauki tawa.” Sai yayan ya amince da maganar ɗan’auta. Sai ɗan’auta ya sami igiya ya ɗaure ciyawar yayan nan tamau, yadda macijin nan ba zai iya motsi ba. Ya yi haka ne domin ya san aljana ce ta zama maciji.

Da kowa ya ɗauki ciyawarsa suka kama hanyar gida, can sun kusa da gari sai suka tarar an hura wuta tana ci ganga-ganga, abin ban tsoro. Sai ɗan’auta ya jefa ciyawarsa a cikin wutar. Da suka ga haka, sai ’yan’uwansa suka ce: “Me ya sa ka jefa ciyawar ka a cikin wuta?” Sai ya ce: “Ku tsaya za ku gani.” Can da wutar ta lafa, sai ya ɗauki kara ya tona ciyawarsa, sai suka ga macijin nan ya ƙone ƙurmus.

Mamakin baiwar ɗan’auta ya kama ’yan’uwansa. Shi kuwa ba abin da ya dame shi; sai yace musu: “Mu tafi gida, daga yanzu ƙaryar aljanar nan ta ƙare.” Wannan ne ya sa a ko ina ake tsoron ’yan bakwai. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Ba kullum akan kwana a kan gado ba.
  • Yawan shekaru ba shi ne wayo ba, Allah na yin baiwarsa ga wanda ya so yaro ne shi ko babba.
  • Mugun nufi ba ya kashe ɗan kurciya.

Danna nan don karanta Tatsuniyar Wata Mayya Da Danta

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar Wata Mayya Da Danta
Labarin na GabaTatsuniyar Wata Mata Da ’Ya’yanta
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.