Tatsuniyar Wata Mata Da ’Ya’yanta

0
7

Ga ta nan, ga ta nanku.

A can kudu da garin su Gizo da Koƙi akwai wata mace mai ’ya’ya mata su huɗu, waɗanda ubansu ɗaya. Suna nan zaune cikin jin daɗi, sai ciwo ya kama mijinta, watau uban yaran nan. Da ya ga kamar ba zai tashi ba, sai ya sa aka yi wa ’yan matan nan huɗu aure. Bayan kamar wata uku da aurar da su, sai ya cika.

Ɗaya daga cikin ’ya’yan nan ta yi aure a garin da ba a barci; ta biyu ta yi aure a garin da ake tsinkar gauta da hanci da tsinkar kuɓewa da ƙirji; ta uku kuma ta yi aure a garin da ba a cin abinci, ba a kashi sai dai a sha romon nama; ta huɗun ta yi aure a garin da ba a kwana a gida sai a can sararin sama. Wata rana sai matar ta shirya za ta ziyarci ’ya’yanta.

Sai ta ɗauki ƙwarya ta kama hanya sai garin ’yarta ta fari, watau garin da ba a barci. Da ta je gidan ’yarta, sai ’yar ta razana ta ce: “Inna me ya kawo ki garin nan da ba a yin barci?” Tun da tana son ganin ɗiyarta, sai ta ce mata: “Ai tun da babanku ya rasu ban sake barci ba.” Sai ’yar ta ce: “To shi ke nan.” Suka zauna ta yi mata abinci ta ci.

Da dare ya yi sai suka kama hira a cikin ɗaki. Can sai uwar ta fara gyangyaɗi. Da ’yar ta ga haka, sai ta ce da gyatumarta: “Kada ki yi barci fa.” Sai ta juya suka cigaba da hirarsu da mijinta. Jiki da jini, can sai uwar ta kwanta ta kama barci. Da mijin ’yar ya lura surukarsa ta kwanta tana barci, sai ya fita ya tara mutane ya ce surukarsa ta rasu.

Da gari ya waye, sai masu haƙa ƙabari suka tafi maƙabarta suka kama aiki. Aka shiga shirye-shiryen binne wannan matar. Data ji hayaniyar mutane, sai ta fito tana yi musu magana, tana cewa ita fa ba ta mutu ba, barci kurum ta yi. To su ba su san barci ba. Sai
wani daga cikin mutanen da suka taru ya ce wa sauran da ke saurarenta: “Yaya kuke magana da fatalwa bayan kun san ta mutu?

Mutum zai mutu ya dawo ne?” Wannan abu ya tsorata matar, saboda haka sai ta koma cikin ɗakin ’yarta; sai ’yarta ta ce: “To kin san na gaya miki ba a barci a nan garin; su ba su san barci ba.” Baƙuwar nan ta rasa yadda za ta yi. Idanu suka raina fata. Can dai wata dabara ta faɗo wa ’yar. Ta dubi uwar ta ce: “Zo in fitar da ke ta danga ki gudu, in ba haka ba za su binne ki da rai.”

Sai ta ja ta suka bi ta bayan gida, ta buɗe mata hanya ta gudu ta nufi garinsu. Bayan kwana ɗaya da komawar matar nan gida, sai ta ce bari ta je garin ’yarta ta biyu, watau garin da ake tsinkar gauta da hanci kuma a tsinki kuɓewa da ƙirji. Sai ta kama hanya har ta isa garin. Da ta isa gidan ’yar, sai ’yar ta ce: “Inna me ya kawo ki nan?

Kin sani fa a nan garin ba a cin abinci. Kowa sai dai ya tsinki kuɓewa da ƙirji, kuma ya tsinki gauta da hanci. Shi ne iyakar abinda mukan ci. Idan kuma ba ki tsinka ba, to kuwa ba za ki ci komai ba.” Da jin haka sai uwar ta ce: “Haba, ai mu ma a garinmu da ƙirji muke tsinkar kuɓewa, sai da na auri babanku na daina.” Sai ’yar ta ce: “To shi ke nan.”

Da yamma ta yi duk sauran matan gida suka ɗunguma gona tsinkar kuɓewa tare da baƙuwar. Kowa ya kama yana tsinka, har suka ƙoshi. Amma baƙuwar nan ba ta tsinka ba, ƙirjinta ko ya dame ta da ƙaiƙayi. Haka ta kwana da yunwa. Washe-gari ma kowa ya tsinki kuɓewa da gauta da ƙirjinsa, amma ban da ita.

Ta sake kwana da yunwa. Da ta ga ta kwana biyu ba ta ci komai ba, sai ta gaya wa ’yar za ta koma gida. Da ’yar ta ji haka, sai ta dubi uwar tace: “To, bari in raka ki.” Sai ta riƙe wa uwarta ƙwaryarta ta raka ta bayan gari, suka yi bankwana, kowa ya koma garin da yake. Da matar nan ta isa gida ta huta kwana ɗaya sai ta shirya ziyartar ’yarta ta uku, watau dai ba ta daddara ba.

’Yar kuwatanacan garin da ba a cin nama ne sai dai romo, domin su zubar danama suke yi idan sun dafa. Sai ta haɗa kayanta, ta kamahanyasai garin ’yarta ta uku. Da ta isa sai ’yar ta yi mamakin ganinta, kuma ta ce da ita, “Inna ba za ki iya zama a garin nan ba fa sabodaa nan ba a cin abinci, ba a yin kashi, kuma ba a cin nama sai dai romon naman.”

To abin ka da wanda ya saba da gardama, sai uwar ta ce: “Haba, ai ni rabona da cin abinci tun sanda babanku ya mutu.” Da ta ji bayanin uwar sai ta ce: “To shi ke nan.” Sai suka zauna. Da lokacin cin abinci ya yi, sai ta ga ’yarta ta dafa nama mai yawa, ta tsiyaye romon, za ta zubar da naman, sai tace: “Haba ’yar nan ai kin gaji, bari in je in zubar miki da shi.” Da ta karɓi nama ta fita bayan gida sai ta zauna ta cinye shi duka.

Bayan ta dawo sai ’yar ta tambaye ta: “Yaya na ga kin daɗe baki dawo ba?” Da uwar ta ji wannan tambaya sai ta ce: “Ai bayan gari na kai.” Sai ’yar ta ce: “To madalla, hakan ya yi.” Can cikin dare sai uwar ta tashi daga barci ta ce wa ’yar tana jin kashi. Sai ’yar ta ce mata: “Ki tuna fa na gaya miki ba a yin kashi a nan garin, shi ya sa ma ba mu da shadda a nan garin.”

Da kashin ya matsanta wa uwar, sai ’yar ta ba ta tukunya ta cika ta da kashi; ’yar kuma ta ɓoye tukunyar kashin. Da gari ya waye sai kajin garin suka kama cara da kuka suna cewa: “Kukuruku, an yi kashi a garin nan.” Idan akuya ma za ta yi kuka sai ta ce: “Be, be, be, an yi kashi a garin nan.” Haka dai duk dabbobi suka dinga yin wannan fallasa a cikin kukansu.

Da abin ya yi yawa sai Sarkin garin ya tara mutanen garinya ce: “Wane ne ya yi kashi a garin nan?” Kowa ya ce bai sani ba. Aka yi ta bincike, kowa yana cewa bai yi kashi ba, kuma ba su san wanda ya yi ba. Da Sarki ya ga magana tana nema ta yi tsawo, sai ya ce: “To za a yi al’adar da aka saba yadda duburar duk wanda ya yi kashin nan za ta riƙa waƙa, kowa ya ji a gari.”

Sarki ya sa aka yi magani; nan take duburar matar nan ta fara waƙa. Da ’yar ta ji sai ta ce: “Inna zo in raka ki domin kada a sani mu ji kunya.” Nan dai a cikin gaggawa ta tattara kayanta, ta raka ta bakin gari suka yi ban kwana ta tafi bayanta na waƙa. Matar nan tana cikin tafiya a dajin da ke tsakanin garin da ta je da wanda za ta, sai ta haɗu da wani Bafulani yana kiwo; sai yace yana son abin nan da ke yin wannan waƙa mai daɗi haka.

Sai tace: “Zan ba ka idan za ka ba ni shanu biyu.” Kamar da wasa sai ya amince da hakan. Ta ce masa ya yi kashi ya shafa mata, abin zai koma jikinsa. Sai ya ba ta shanu biyu, kuma ya yi kashi ya dangwala ya shafa mata. A nan take abin ya koma jikinsa, yana waƙa. Sai ya shiga daji da shanunsa yana murna.

Ita kuwa ta kora shanunta biyu ta shiga gari, ta je gida ta ɗaure kayanta. Bayan kwana biyu sai matar nan ta shiga shirin zuwa wurin ɗaya ’yarta wadda a garin da take aure ake kwana a sama. Shi kenan ta ɗau hanya, tana isa garin ta zarce gidan auren ’yarta. Da ta ga uwarta ta yi murna, amma sai ta ce mata: “Sai dai fa mu a nan garin idan dare ya yi muna tashi sama mu kwana a can ne saboda mayu suna yawan zuwa nan.”

Sai uwar ta ce: “Ai babu komai, zan yi tsalle in hau sama kamar yadda kowa zai yi.” A nan ne fa ’yar ta ce: “To yi tsallen mu gani.” Kamar da gaske, uwar ta fara gwadawa. Da ta ɗaga ƙafa sai ta faɗi, ta yi ta yi, har ta gaji, kuma ga shi dare ya yi. Tun da an riga an makaro, sai ’yar ta ce wa uwar: “Zan ɓoye ki a cikin ɗaki, amma kada ki yi magana ko da za ki ji ana ta buɗe-buɗe da bincike a ɗakin.

Domin mayun ne ke neman mutanen da ke kwana a ƙasa su cinye.” Uwar ta amsa mata cewa ba za ta yi magana ba. Can matar tana kwance a ɗaki sai ta ji motsi da ɓuruntu. Sai ta manta da dokar da ’yar ta sa mata ta rashin magana, ta ce: “Wane nenan?” Kafin ta gama rufe baki mayun nan sun afka kanta, sun cinye ta. Kurunkus.

Abubuwan Da Labarin Yake Koyarwa

  • Idan ka baƙunci gari ka tarar da mutan garin kowa da wutsiya to kai ma ka sami zangarniya ka saka, sai ka zauna lafiya.
  • Wanda bai ji bari ba, ya ji hoho.
  • Da muguwar rawa, gwamma ƙin tashi

Danna nan don karanta Tatsuniyar ‘Yan Bakwai Da Aljana

Wannan tatsuniya an ciro ta ne daga littafin TASKAR TATSUNIYOYI wanda Bukar Usman OON ya wallafa.

Edita@rumasau-kallamu

labarin da ya wuceTatsuniyar ‘Yan Bakwai Da Aljana
Labarin na GabaTatsuniyar ‘Yan Goma Sha Ɗaya
wikiHausa
wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.