Ilimi kalmar Balarabiya ce da ke nufin ‘sani’, amma a nan za mu ba shi ma’ana biyu, tarbiyar sanin ilimi (education) da kuma ilimin kansa (knowledge).
Kafin zuwan addinin Musulunci da Turawa, Bahaushe na ba wa al’ummarsa ilimi da tarbiyyar da baka (orature), ta hanyar tarihi, tarihihi, tatsuniya, maganganun hikimi (karin magana da azanci) domin tashi da xabi’u na gari da sanin dabarun zaman duniya.
Rubutun Ajami
Bahaushe ya fara rubutun zube bayan zuwan Larabawa da addinin Musulunci Bahaushe ya fara amfani da rubutun ‘Ajami’ (Arabic script). Bahaushe na rubutun Hausa cikin haruffan Larabci (Bunza, 2002), tun kafin zuwan rubutu boko (Latin script) kusan shekuru dubu da xari xaya (1100) tun lokacin zuwan Bayajidda a wasu yankunan.
Domin Karanta Ma’anar Bahaushe Danna nan
An fara amfani da ‘ajami’ tun shigowar addinin Musulunci a qarni na goma sha uku a lokacin Sarkin Kano Naguji (1194 – 1247) har izuwa zuwa lokacin zuwan Wangara qasar Kano (Magaji, 1982 da Malumfashi, 2009).
Rubutun Boko
Bayan zuwan Turawa a 1912, Hausawa suka ci gaba adana adabinsu da baqaqen boko (Latin script), har zuwa yau. An sami Turawa da suka zauna suka koyi harshen Hausa da nazarin Harshen kamar C.H. Robinson, W.R. Miller, Richardson, F. Edgar, Ryder da Burgin da Tripoli ta qasar Libya , har suka yi rubuce-rubuce kan nahwun harshen Hausa (Ekkahard, 1998).
Bayan nan, Bahaushe na iya karatun zamani (boko) na likitanci, siyasa, hukunci, zamantakewa da tattali a kowanne mataki a ciki da wajen qasar Hausa. Bahaushe yana aiki da iliminsa domin koyarwa a makarantu, aikin gwamnati, tsaro da rubuce-rubuce har zuwa yau.
Domin Karanta Al’adar Bahaushe Danna nan
Almajiranci
Kalmar almajiranci an juyo ta ne daga kalmar harshen Larabci ‘almuhajir’ ma’ana ‘xan hijiri/qaura’. Almajiranci daxaxxiyar al’adar neman ilimi ce, mutum zai tashi daga gari zuwa wani gari don neman ilimi, ba ga iya Hausawa ba, sai dai ‘yan bambance-bambance da ta wasu wurare, da zamanantarwa musamman a qasashen Gabas ta Tsakiya, da Pakistan, da Sudan da Somaliyya ta Afrika. A qasar Hausa, an fara almajiranci bayan zuwan Wangarawa Kano a zamanin sarkin Kano Yaji xan Tsamiya (1349 – 1385). A Katsina kuma, bayan zuwan Sheik Abdurrahman Zaite a lokacin sarki Muhammad Korau (1384 – 1398).
Domin Karanta wane ne bahaushe Danna Nan
Makarantar allo ko ‘tsangaya’, nan ne muhalli da ake koyo da koyar da Alqur’ani Mai girma, a wasu wuraren, ana haxe da karatun sauran littafan addinin Musulunci. Wasu na tasowa daga garuruwa, su xauki shekaru suna karatu (boarding), wasu kuma daga gidajensu suke zuwa (day). Yawanci ana karatu bayan sallar Asubah, lokacin hantsi, bayan sallar Azahar da La’asar da Isha’i, a wasu wuraren hadda bayan Magriba. Yawanci ana bada hutu a ranakun Alhamis da Juma’a.
Karatun almajiranci yana da matakai goma sha xaya (kamar matakin aji) daga gwaji, sai babbaku, farfaru, hajjatu, sare, ture, satu, karya takarda, shan fari, gwani, gangaran (ma’ana, mutum ya haddace, ya iya rubuta Alqur’ani Mai girma da ka).
Makarantar allo na qarqashin shugabancin Uban Tsangaya, sai mai taimaka sa Maidarasu, sai shugaban xalibai (shugaban gardawa). Sannan akwai tsarin horarswa ga wanda ya yi laifi, ko ya gudu. Bayan ‘yan shekaru, ana qoqarin koyar da gardawa da qolawa sana’o’in hannu na dogaro da kai, kamar saqar tufa ko hula, rini, noma da sauransu.
[…] Danna nan don karanta zuwan ilimi ƙasar Hausa […]