Adabin Bahaushe

0
27

Adabi kalmar Larabci ce da ke nufin al’ada. Al’ada ta  qunshi dukkan abubuwan da al’aumma ke yi waxanda  suka haxa da ilimi, imani, fasaha, qere-qere, tarbiyya da  sauran halayyen xan Adam (Talyor, 1871). Aristotle  (384 – 322BC) al’ada madubin rayuwa ce. 

Ubali (2021) Bahaushe na da al’adu ta jiyau da ganau.  Jiyau ita ce al’adar da take cikin tunani, ko ake ji da  kunne, kamar zumunci, kunya, faxa, kishi da sauransu.  Ganau kuma ita al’adar da ake iya gani da ido, ko yi  aikace da gavvan jiki, kamar tufafi, sa’ana, haihuwa da  sauransu. 

Domin Karanta Ma’anar Bahaushe Danna nan 

Amma a nan, adabi ana nufi fasahar qirqira ta harshe  cikin tsarin labari, waqe ko kwaikwayon rayuwar zahiri  domin koyar da al’umma tsarin rayuwa mai kyau. Kafin  zuwan rubutu suna adana adabinsu da baka, wannan dalili ya sa tarihi da adabin Bahaushe da yawa suka  salwanta. Kafin zuwan rubutu qasar Hausa, Bahaushe na  amfani da harshe wajen sadar da baka/ka (orature a  Turance, oral + literature = ora(l litera)ture). Wasu  kuma suna amfani da duma, fatun dabbobi, ko dutse, ko wata masaida a jikin mutum. 

Amfanin adabin baka ga al’ummar Hausawa a wancan  lokaci ana jiyar da yara tarihi, bada tarbiyya cikin  labarun tatsuniyoyi, tarihi, tarihihi, hikaya, al’amara,  karin magana, salon magana, take da qirari, zaurance,  don yaxa martabar Hausa da xabi’unsu, ko wasa  kwakwalwa da gagara gwari (tongue twister), nishaxi,  gina tunani da falsafar rayuwar Hausawa duk da harshen  Hausa (Xangambo, 2008). 

Domin Karanta Al’adar Bahaushe Danna nan 

Ta vangare waqa da kixa Bahaushe yana, mawaqa da  makaxan fada (mis., Xankwairo), makaxan sana’a,  makaxan jama’a (misali, Mamman Shata da Haruna Uji),  makaxan maza (mis. Gambo Fagada), makaxan mata  (mis. Barmana Coge da Mai Amada).

A wajen kixa  Bahaushe na amfani da goge, kalangu, gurmi, kuntigi,  garaya, tafi, qaho, jauje, gula, ganga, duman girke,  kotso, tambari, kwarya, akayau da kayan bushe-bushe  irin su algaita, qaho, kakaki, farai da sauransu (Gusau,  2008). Bahaushe yana da sauran waqoqi da yake a  lokacin aikin gona, aikin gayya, yaqi, ko yara a wajen  wasa, kamar ‘yargalala ta mata da sauransu.  BAHAUSHE na amfani da kixi da waqa, ko waqe domin zuga, jinjina, qara qaimi, zambo, faxakarwa, ko  isar da wani saqo.  

Domin Karanta wane ne bahaushe Danna Nan

Bahaushe yana wasan kwaiwayo na gauta da ake a fadar  sarakuna, yana kwaikwayon hawan dokin kara, da tashe  bayan zuwan addinin Musulunci don nishaxi da  faxakarwa.

Domin karanta cikekken littafin Danna nan 
labarin da ya wuceHarshen Bahaushe (Harshen Hausa)
Labarin na GabaZuwan Ilimi Qasar Hausa