A yau za mu koyi yadda ake shinkafa ‘yar Senegal. Shinkafa ‘yar Senegal na da matuƙar daɗi.
Abubuwan Da Ake Buƙata
- Shinkafa
- Karas
- Koren wake
- Tattasai
- Attaruhu
- Albasa
- Niƙaƙƙen nama
- Magi
- Kori
- Garin tafarnuwa da citta
Yadda Ake Haɗawa
- A ɗora tukunya da ruwa a cikinta, har sai ya tafasa, sannan a ɗauko shinkafa ’yar wara a wanke a zuba a ciki.
- Idan ta ɗan tafasa kamar na minti 10 zuwa 15, sai a sauke a wanke da ruwa a tsame ta a matsami ruwan ya tsane.
- Sannan a samu ɗanyen nama a niƙa shi. Naman ya kasance da ɗan yawa.
- A sake ɗora wata tukunyar a wuta sannan a zuba man gyaɗa a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai.
- Sannan sai a zuba niƙaƙƙen naman a ciki, a ci gaba da soya shi, sannan a ɗauko garin citta da tafarnuwa da magi da kori sai a ci gaba da gaurayawa.
- Sannan a zuba su karas da koren tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da marufi na tsawon minti 20 sannan a sauke.
- A samu salad a yayyanka a dafa ƙwai a zuba “cream” sannan a ɗora a ci, ita da jus ɗin lemo.
Domin sanin yadda ake sharbar dankali danna nan