Tag: shinkafa

  • Yadda Ake Shinkafa ‘Yar Senegal

    Yadda Ake Shinkafa ‘Yar Senegal

    A yau za mu koyi yadda ake shinkafa ‘yar Senegal. Shinkafa ‘yar Senegal na da matuƙar daɗi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Shinkafa
    • Karas
    • Koren wake
    • Tattasai
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Niƙaƙƙen nama
    • Magi
    • Kori
    • Garin tafarnuwa da citta

    Yadda Ake Haɗawa

    1. A ɗora tukunya da ruwa a cikinta, har sai ya tafasa, sannan a ɗauko shinkafa ’yar wara a wanke a zuba a ciki.
    2. Idan ta ɗan tafasa kamar na minti 10 zuwa 15, sai a sauke a wanke da ruwa a tsame ta a matsami ruwan ya tsane.
    3. Sannan a samu ɗanyen nama a niƙa shi. Naman ya kasance da ɗan yawa.
    4. A sake ɗora wata tukunyar a wuta sannan a zuba man gyaɗa a yayyanka albasa a zuba ta soyu sosai.
    5. Sannan sai a zuba niƙaƙƙen naman a ciki, a ci gaba da soya shi, sannan a ɗauko garin citta da tafarnuwa da magi da kori sai a ci gaba da gaurayawa.
    6. Sannan a zuba su karas da koren tattasai da attarugu da shinkafar sannan sai a gauraya sai a rage wuta a rufe tukunyar da marufi na tsawon minti 20 sannan a sauke.
    7. A samu salad a yayyanka a dafa ƙwai a zuba “cream” sannan a ɗora a ci, ita da jus ɗin lemo.

    Domin sanin yadda ake sharbar dankali danna nan

  • Yadda Ake Yin Alalan Shinkafa

    Yadda Ake Yin Alalan Shinkafa

    A yau zamu koyi yadda ake alalan shinkafa.

    Abubuwan Da Ake Buƙata:

    • Shinkafa ta tuwo
    • Ƙwai
    • Nama
    • Hanta
    • Attaruhu
    • Albasa
    • Magi
    • Gishiri
    • Curry
    • Main gyaɗa

    Yadda Ake Haɗawa:

    1. A wanke shinkafa a shanya ta, ta bushe a kai a niƙa ta.
    2. A tankaɗe a kwaɓa da ruwa kamar ƙullun alala, a jajjaga attaruhu a zuba a yanka albasa a zuba a yanka dafaffiyar hanta ƙanana a zuba, a daka dafaffen naman a zuba.
    3. A zuba dafaffen ƙwai da aka yanka, a zuba maggi da gishiri da curry a sa mai yadda zai yi.
    4. Sai a jujjuya a zuba a leda a dafa kamar alala, idan kuma na gwangwani za a yi, sai a zuba mai a jikin gwangwani a zuba ƙullun a turara shi, idan ya yi, sai a kwashe a zuba filas.

    Domin karanta Yadda Ake Faten Wake Da Doya ko Yadda Ake Tsaba Da Wake danna koren rubutu.