Yadda Ma’anar Roƙo Take

0
553

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya (2006:374), ta bayyana roƙo da cewa; “Sana’ar maroƙa ta yi wa mutane kirari ko yabo don a yi musu kyauta” Ko kuwa, “Neman kyauta daga wani”.

Kenan roƙo, wata dabara ce ta neman abu a hannun wani ta hanyar zuga shi da yi masa kirari da yabon kyawawan halayensa; a wani lokacin ma da ƙoƙarin ƙarin gishiri kan halin da ba nasa ba.

Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Wayon Roƙo a Adabin Baka; Nazarin Roƙo a Wasu Waƙoƙin Kamilu Almajirin Mawaƙa wanda Ibrahin Baba (Nayaya) ya wallafa shi.

Domin karanta cikakken bayani a kan Taƙaitaccen Tarihin Kamilu Almajirin Mawaƙa danna nan

Domin karanta bayani akan Kasuwanci Da Fatauci A Ƙasar Hausa danna nan

labarin da ya wuceTaƙaitaccen Tarihin Kamilu Almajirin Mawaƙa
Labarin na GabaYabo Daga Waƙar Maryam Fantimoti