Ko Kunsan Cewa Uwa Zata Iya Samun Juna Biyu Bayan Sati Shida Da Haihuwa

0
66

Nasan tambayar da zaizo muku shine tayaya zaku kare kanku daga samun cikin da baku shirya ba bayan haihuwa.

Ga Hanyar:

Da zarar an haihu ma’urata ku yi amfani da hanyar shayar da nonon uwa zalla ba tare da an hada da abinci ko ruwa ba,sannna kuma ma’aurata su fara amfani da wata hanyar bada tazarar haihuwa bayan shayar da nonon uwa zalla,zai kara taimaka wajen tabbatar da bada tazarar haihuwa cikin koshin lafiya,akalla idan mace ta haihu ana buƙatar tazarar shekara guda zuwa biyu kafin daukar wani cikin.

Ga kadan daga cikin amfanin tazarar haihuwa ga iyaye mata da yaransu:
  • Yana karawa yaro/yara annashuwa,sakamakon kulawar da suke samu daga wajen iyayensu.
  • Yana sa yara su samu kulawa ta ɓangaren lafiyarsu da kuma samun ingantaccen ilmi.
  • Mace za ta samu isasshiyar dama wajen cigaba da rayuwarta,sannan ta taimaka wajen bunƙasa cigaban iyalinta.
  • Mace za ta samu isasshen lokacin kula da mijinta da kuma samun ƙarin danƙon soyayya.
  • Yana rage damuwa da kasala ga mata a gidajensu.
  • Za tabawa mace damar shayar da jaririnta na tsawon lokaci,inda yin hakan kan ba da kariya daga cututtuka da dama.
  • Tazarar haihuwa kan baiwa maigida damar kulawa da iyalansa yadda ya kamata.
  • Maigida yakan samu ƙarancin damuwa da kasala a rayuwarsa ta yau da gobe.
  • Haka nan zai samu isasshen lokacin zama da iyalinsa a gida da kuma ba su tarbiyyar da ta dace.
  • Zai ba wa maigida damar sauke nauyin da ke kansa na tarbiyya da sauran haƙƙoƙin da ke wuyansa na rayuwar ‘ya’yansa.

Domin karanta Halayen Dake Haddasa Lalacewar Ƙoda [Kinney Dx] Danna nan

labarin da ya wuceHalayen Dake Haddasa Lalacewar Ƙoda [Kinney Dx]
Labarin na GabaAlamomi Masu Hatsari Lokocin Juna Biyu