Terms Dictionary

Farmaki - Tana nufin kai hari ba zato ba tsammani. Misali; 'Yan ta'adda sun kai farmaki ga jami'an tsaro. ENG; Sudden Attack (A turance tana nufin farmaki)
Fartanya - Tana nufin wani ƙarfe mai ƙota da ake amfani da shi don yin noma. Misali; Ado ya saɓa fartanya ya nufi gona. ENG; Hoe (A turance tana nufin fartanya)
Fasaha - Azancin kirkirar wani abu mai amfani ga rayuwar dan'adam ko dabarar sarrafa tunani domin nishaɗantarwa
Fasahar Bayanai - Azancin sarrafa ko dabarar tsara bayanai
Fasahar Sadarwa - Kusan fusan fasahar bayanai ce.
Fasahar Sana’a - Dabarar sarrafa tunani wajen aiwatar da aikin ko sana'o'in hannu.
Fassara - Tana nufin daga wani harshe zuwa wani harshe. Misali; Ya fassara littafin daga harshen larabci zuwa harshen Hausa. ENG; Translation (A turance tana nufin fassara)  
Fasting - A turance yana nufin azumi.  Misali; Ranar litinin zan yi azumi idan Allah ya kai mu. HAU; Azumi (Yana nufin barin ci da sha da mu'amalar auratayya tun daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana)
Fasto - Tana nufin limamin coci. Misali; Maƙococinsa babban fasto ne. ENG; Pastor (A turance tana nufin fasto)
Fat - A turance tana nufin ɓulele. Misali; Sabon ɗalibin da aka kawo mana ɓulele ne. HAU; Ɓulele (Tana nufin mai ƙiba)
1 95 96 97 98 99 300