Duhu - Tana nufin rashin haske.
Misali; Gari ya yi duhu sakamakon hadarin da ya haɗo.
ENG; Darkness (A turance tana nufin duhu)
Dull - A turance tana nufin daƙiƙi.
Misali; Sun ce masa daƙiƙi saboda ya faɗi jarrabawa.
HAU; Daƙiƙi (Tana nufin wanda ba ya gane karatu)
Dung beetle - A turance tana nufin buzuzu.
Misali; Buzuzu ya fito a ƙofar gidan shi yasa ba zan iya shiga ba.
HAU; Buzuzu (Tana nufin wani nau'in ƙwaro mai tashi)
Dutse - Tana nufin dunƙulallun halittun Allah da ke doron ƙasa.
Misali; Akwai gungumemen dutse a garin mu.
ENG; Stone (A turance tana nufin dutse)
Dye-pit - A turance tana nufin karofi.
Misali; Na taɓa ganin karofi a marinar da ke unguwar Ƙofar Mata.
HAU; Karofi (Tana nufin rami mai ɗauke da ruwan da ake rina tufafi)
Dysentary - A turance yana nufin atini.
Misali; Yara kan yi atini sakamakon shan zaƙi da suke yi.
HAU; Atini (Yana nufin ba-haya mai danƙo kuma mai wahalar fita wanda shan zaƙi ke haddasawa)
Ear - A turance tana nufin kunne.
Misali; Yara na yawan yin ciwon kunne musamman lokacin sanyi.
HAU; Kunne (Tana nufin gaɓar da ake ji da ita)
Economic Financial Crime Commission (EFCC) - Hukumar hana ta'adin tattalin arziki
Eczema - A turance tana nufin kirci.
Misali; Abin da yasa almajirai suke yin kirci shi ne rashin wanka.
HAU; Kirci (Tana nufin wasu ƙuraje masu matuƙar ƙaiƙayi da ke fitowa a fata sakamakon rashin tsabta)
Education Trust Funds (ETF) - Asusun Tallafawa llimi