Terms Dictionary

Daƙiƙi - Tana nufin wanda ba ya gane karatu. Misali; Sun ce masa daƙiƙi saboda ya faɗi jarrabawa. ENG; Dull (A turance tana nufin daƙiƙi)
Daƙuwa - Tana nufin alawar da ake yin ta da niƙaƙƙiyar gyaɗa da aya da sikari. Misali; Zan kai wa amarya daƙuwa saboda idan ta yi baƙi ta ba su. ENG; Sweet made from ground tigernuts and groundnut (A turance tana nufin daƙuwa)
Daƙwalwa - Tana nufin babbar kaza ma'abociyar tsoka. Misali; Kazar daƙwalwa ce don ta ƙosar da mu. ENG; Large hen (A turance tana nufin daƙwalwa)
Deaf person - A turance tana nufin kurma. Misali; Tun yana yaro ya zama kurma sakamakon ciwon baƙon dauro da ya yi. HAU: Kurma (Tana nufin mai ɗauke da lalurar rashin ji)
Death (of prophets or saints) - A turance tana nufin faku. Misali; Ba su san annabi ya faku ba. HAU; Faku (Tana nufin mutuwar annabawa ko bayin Allah salihai)
Debt - A turance tana nufin bashi. Misali; A bashi ya karɓo kayan gininsa. HAU; Bashi (Tana nufin karɓar kuɗi ko wani abu da zimmar biya daga baya)
Debt Management Office (DMO) - Ofishin harkokin bashi
December - A turance yana nufin wata na ƙarshe a shekara.  Misali; Watan Disamba yana da kwana talatin da ɗaya. HAU; Dismba (Wata ne na ƙarshe a shekara)
Defense Intelligence Agency (DLA) - Hukumar leƙen asiri ta soji
Delay - A turance tana nufin jinkiri. Misali; An samu jinkiri wajen fitar da sakamakon jarrabawar saboda wasu ƙwararan dalilai. HAU; Jinkiri (Tana nufin dakatawa ko ɗaukan lokaci)
1 80 81 82 83 84 300