Accident Investigation Bureau (AIB) - Hukumar Binciken Haɗura
Acting in a careless way - A turance tana nufin ganganci.
Misali; Tuƙin gangancin da direban yake yi ne ya janyo hatsarin.
HAU; Ganganci (Tana nufin yin abu ba tare da kula ba ko gaba-gaɗi)
Actors Guild of Nigeria (AGN) - Kadaurar Jaruman Fim Ta Najeriya
Adabi - Yana nufin madubin duba rayuwar al'umma.
Misali; Adabin Hausa yana da faɗi da rassa daban-daban.
ENG; Literature (A turance yana nufin Adabi)
Adadi - Yana nufin yawan abu.
Misali; Kirkin Malam ba shi da adadi.
ENG;Sum/Total (A turance yana nufin adadi)
Adda - Makami ne mai ƙota da ake amfani da shi a gona da sauransu.
Misali; Ya sare bishiyar da adda yau da safe.
ENG; Matchet (A turance yana nufin matchet)
Adiko - Maɗaurin kai na mata.
Misali; Kande ta ɗaure kai da adiko.
ENG; Head-tie (A turance yana nufin maɗaurin kai na mata)
Administer - A turance tana nufin gudanar.
Misali; An gudanar da taron a gidan adana ababen tarihi.
HAU; Gudanar (Tana nufin aiwatarwa)
Administration - Ma'aikata, Mulki
Administrative Staff College Of Nigeria (ASCON) - Kwalejin Jami'an Ma'aikata Ta Najeriya