Terms Dictionary

Ɗaci - Tana nufin wani yanayi mara daɗi da ake ji a maƙogwaro idan an ɗanɗana abubuwa kamar magani da sauransu. Misali; Maganin yana da ɗaci sosai. ENG; Bitterness (A turance tana nufin ɗaci)
Ɗaukaci - Dukkani, Gabadaya, Kafatani
Ɗauraye - Tana nufin sa ruwa a sake wanke abu. Misali; Na ɗauraye kwanon kafin in zuba abinci. ENG; Rinse (A turance tana nufin ɗauraye)
Ɗawafi - Tana nufin zagaye Ka'aba da zimmar ibada. Misali; Duk wanda ya je Umara sai ya yi ɗawafi. ENG; Circle the Ka'aba at Macca (A turance tana nufin ɗawafi)
Ɗazu - Tana nufin lokacin da be daɗe da wucewa ba. Misali; Ɗazu na dawo daga gidan bikin. ENG; A moment ago (A turance tana nufin ɗazu) Kishiyarsa; Yanzu
Ɗaɗɗoya - Tana nufin wani ganye mai ƙamshi wanda ake magani da shi. Misali; An yi amfani da ganyen ɗaɗɗoya wajen haɗa maganin. ENG; A fragrant herb (A turance tana nufin ɗaɗɗoya)
Ɗigil - Tana nufin ɗan gajere ko ƙanƙani. Misali; Na ga wani ɗan ɗigil a kasuwa yau. ENG; Very Short (A turance tana nufin ɗigil)
Ɗimbi - Tana nufin da yawa. Misali; Muna miƙa godiya mai ɗimbin yawa ga waɗanda suka samu damar zuwa taron buɗe kamfaninmu. ENG; Superabundance (A turance tana nufin ɗimbi)
Ɗingishi - Tana nufin yin tafiya ba daidai ba, ana yi ana dakatawa saboda dalilin ciwo a ƙafa ko wani abu daban. Msali; Ɗingishi take yi saboda marurun da ya fito a ƙafarta. ENG; Limping (A turance tana nufin ɗingishi)
Ɗoyi - Tana nufin tsananin wari. Misali; Kwatar ɗoyi take tun safe da aka kwashe. ENG; Stench (A turance tana nufin ɗoyi)
1 297 298 299 300