Terms Dictionary

Type of cloth without embroidery - A turance tana  nufin gare. Misali;Malam Audu ya sa gare. HAU; Gare (Tana nufin rigar Hausawa mara ado)
Ulcerated Wound - A turance tana nufin gyambo. Misali; Ai gyambon da ke ƙafarsa ya daɗe sosai. HAU; Gyambo (Tana nufin ciwon da ba ya warkewa ko kuma ya daɗe bai warke ba)
Uncle - A turance tana nufin kawu. Misali; A cikin mutanen da suka zo har da Kawu, shi ne ma ya jagoranci tafiyar. HAU; Kawu (Tana nufin wa ko ƙanin mahaifi ko mahaifiya)
Uncompleted Building - A turance tana nufin kango. Misali; Har yanzu ginin kango ne ba a ƙarasa ba. HAU; Kango (Tana nufin ginin da ba a kammala ba)
Understand - A turance tana nufin gane. Misali; Ina fatan kun gane abinda nake nufi? HAU; Gane (Tana nufin fahimta) Kishiyarta; Rashin Ganewa
Understand - A turance tana nufin fahimta. Misali; Ɗaliban suna da fahimta ƙwarai da gaske. HAU; Fahimta (Tana nufin ganewa) Kishiyarta; Rashin Fahimta
Ungrateful - A turance tana nufin butulu Misali; Cindo butulu ne saboda ya butulcewa maigidansa a kasuwa. HAU; Butulu (Tana nufin wanda yake manta alkahairin da aka yi masa)
Union - Tarayya, Gamayya, Ƙungiya
United Labour Congress (ULC) - Gamayyar Ƙungiyoyin Ƙwadago
United Nations (UN) - Majilisar Ɗinkin Duniya
1 284 285 286 287 288 300