Teach - A turance tana nufin koyar.
Misali; Malam Musa Ya koyar da mu darasin lissafi.
HAU; Koyar (Tana nufin sanar da mutum ilimi)
Teach - A turance tana nufin koyarwa.
Misali; Ya karantar da mu darussa masu yawa.
HAU; Karantar (Tana nufin koyarwa)
Teachres Registration Council of Nigeria (TRCN) - Hukumar Malaman Makaranta Ta Najeriya
Teburi - Teburi wani kayan aiki ne wanda ake amfani dashi wajen rubutu ko kuma ajiye kaya akai musamman a makaranta ko kuma a gida don yin amfani.
Jam'i ; Tebura
Technology Incubation Centre (TIC) - Cibiyar Rainon Fasahar Ƙere ƙere Ta Ƙasa
Ten - A turance tana nufin goma.
Misali; Littattafai goma ne a cikin jakar.
HAU; Goma (Tana nufin lambar da ke bin bayan tara)
Tending animal at pasture - A turance tana nufin kiwo.
Misali; Sana'ar kiwo ta karɓi Malam Iro, garkensa sai haɓaka yake kullum.
HAU; Kiwo (Tana nufin ciyar da dabbobi kamar awaki da shanu da kaji da sauransu)
Termites - A turance tana nufin gara.
Misali; Gara ta cinye kujerun duk sun lalace.
HAU; Gara (Tana nufin ƙwaron da yake cinye katako)
Tertiary Education Trust Fund (TETFund) - Asusun Bunƙasa llimin Mayan Makarantu
Thanks - A turance tana nufin godiya.
Misali; Mun yi wa babanmu godiya ranar da ya siyo mana kayan salla.
HAU: Godiya (Tana nufin yabawa)
Kishiyarta; Rashin Godiya